TAIMAKO DON IYALI
Yadda Ma’aurata Za Su Rika Nuna Kauna Ga Juna
Da shigewar lokaci, wasu ma’aurata na rage yadda suke nuna wa juna kauna. Idan hakan yana faruwa a aurenku, ya kamata ku damu ne?
Abin da ya kamata ka sani
Kauna tana da muhimmanci don aure ta yi karfi. Kamar yadda jikinmu ke bukatar abinci da ruwa a kowane lokaci don mu samu koshin lafiya, haka ma yake da aure. Domin aure ta yi karfi, dole a rika nuna kauna a dukan lokaci. Ko da sun yi shekaru da yawa da yin aure, ma’aurata suna bukatar su rika gaya wa juna cewa suna kaunar juna sosai.
Kauna ta gaskiya ba ta son kai. Amma irin wannan kaunar tana sa aboki ko abokiyar aure farin ciki. Maimakon ka jira sai lokacin da ka ga dama kafin ka nuna wa matarka kana son ta, ya kamata ka san cewa matarka tana bukatar kauna kuma zai dace ka rika nuna mata kana son ta.
Mata suna bukatar a rika gaya musu ana son su fiye da maza. Zai iya yiwuwa miji na kaunar matarsa sosai. Amma idan sai a lokacin da yake bukatar wani abu daga wurinta, kafin ya nuna yana son ta, matarsa za ta rika shakka ko yana son ta da gaske. Yana da kyau a rika nuna kauna a dukan lokaci.
Abin da za ka iya yi
Ka rika yin amfani da kalaman soyayya. Matarka za ta ji kana kaunar ta sosai idan ka yi amfani da kalamai kamar su “Ina son ki” ko kuma “In ba ke ba sai rijiya.”
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Abin da yake cikin zuciya, shi yake fitowa a baki.”—Matiyu 12:34.
Shawara: Ba da baki kawai za ku nuna wa juna kauna ba. Za ku iya nuna hakan ta tura wa juna sakon imel ko tes.
Halayenku su nuna cewa kuna kaunar juna. Idan ka ce “Ina son ki, ka nuna hakan ta wurin rungumar ta ko ka sumbace ta ko kuma ka rike hannun ta. Wata hanya kuma da za ku nuna kauna ga juna ita ce ta wurin taba juna ko yi wa juna kallon soyayya ko kuma ba wa juna kyauta. Yana da kyau ka yi wa matarka wasu abubuwa masu kyau kamar su, rike mata jaka, bude mata kofa, wanke kwanuka ko wanke mata kaya ko kuma dafa abinci. Ga wasu mutane, yin wadannan abubuwan hanya ce da suke nuna suna kaunar matarsu.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku nuna kaunarku ta wurin surutun baki kawai, amma ku nuna kaunarku ta wurin aikatawa.”—1 Yohanna 3:18.
Shawara: Ku nuna kauna ga juna kamar yadda kuka yi a lokacin da kuke fita zance.
Ku rika kasancewa tare. Kasancewa tare zai karfafa aurenku kuma yana tabbatar wa miji ko mata cewa tana jin dadin kasancewarku tare. Hakan na iya zama kalubale idan akwai yara a gida ko kuma idan akwai ayyukan kasuwanci da yawa da ake yi a kowace rana. Idan haka ne, za ku iya yin shiri don ku yi abu mai sauki kamar zuwa yawo tare.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wannan zai taimake ku ku iya zabar abin da ya fi kyau.”—Filibiyawa 1:10.
Shawara: Wasu ma’aurata da suka shagala da aiki, sukan kebe wasu ranaku don fita zance da dare ko a karshen mako.
Ku san juna sosai. Kowane mutum yana da hanyar da yake so a nuna masa kauna. Don haka, ku tattauna don ku san yadda za ku iya nuna wa juna kauna. Ku tuna cewa don aure ta yi karfi, nuna kauna yana da muhimmanci.
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kauna . . . ba ta sonkai.”—1 Korintiyawa 13:4, 5.
Shawara: Maimakon ku rika son a nuna muku kauna, ku tambayi kanku: ‘Mene ne zan yi don matata ko mijina ya nuna mini yana kauna ta?’