Koma ka ga abin da ke ciki

Gabatarwar Littattafan Littafi Mai Tsarki

Wadannan gajerun bidiyoyin suna taimaka mana da bayanai game da littattafan Littafi Mai Tsarki. Ka yi amfani da wadannan darussa don ka inganta yadda kake karanta da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki.

Gabatarwar Littafin Farawa

Littafin Farawa ya gaya mana yadda ’yan Adam suka soma rayuwa da kuma yadda aka soma wahala da mutuwa.

Gabatarwar Littafin Fitowa

Ka ga yadda Allah ya ceto Isra’ilawa daga bauta a Masar kuma ya kebe su a matsayin al’ummarsa.

Gabatarwar Littafin Firistoci

Ka ga yadda littafin Firistoci ya kwatanta yadda Allah yake da tsarki da kuma dalilin da ya sa yake da muhimmanci mu ma mu kasance da tsarki.

Gabatarwar Littafin Joshuwa

Za ka ga yadda al’ummar Isra’ila suka mallaki kasashen da Jehobah ya ba su kuma aka raba wa kabilun filayensu.

Gabatarwar Littafin Alkalai

An samo sunan wannan littafin ne daga maza masu karfin zuciya da Allah ya yi amfani da su don ya ceci Isra’ilawa daga abokan gābansu.

Gabatarwar Littafin Rut

A Littafin Rut an tattauna yadda wata gwauruwa ta nuna wa surkuwarta da gwauruwa ce kauna da kuma yadda Jehobah ya albarkace su.

Gabatarwar Littafin 1 Sama’ila

Ka lura da yadda labarin Isra’ilawa ya canja daga zamanin alkalai zuwa lokacin sarakuna.

Gabatarwar Littafin Ezra

Jehobah ya cika alkawarinsa cewa zai ceci bayinsa daga bauta a Babila kuma ya maido da bauta ta gaskiya a Urushalima.

Gabatarwar Littafin Nehemiya

Littafin Nehemiya yana dauke da muhimman darussa ga dukan bayin Allah a yau.

Gabatarwar Littafin Esther

Abubuwan da suka faru a zamanin Esther zai karfafa bangaskiyarmu cewa Jehobah zai iya ʼyantar da bayinsa a yau daga gwaji.

Gabatarwar Littafin Ayuba

Dukan wadanda suke kaunar Jehobah za su fuskanci gwaji. Labarin Ayuba ya tabbatar mana da cewa za mu iya rike aminci kuma mu goyi bayan sarautar Jehobah.

Gabatarwar Littafin Zabura

Zabura ta goyi bayan Jehobah a matsayin madaukakin sarki, tana taimaka da kuma karfafa masu kaunarsa kuma tana nuna yadda Mulkinsa za ta kawo canji a duniya.

Gabatarwar Littafin Misalai

Ka sami ja-gorar Allah game da batun kasuwanci da na iyali.

Gabatarwar Littafin Mai-Wa’azi

Sarki Sulemanu ya nuna abubuwan da ke da muhimmanci sosai a rayuwa kuma ya gwada su da wadanda ke saba wa hidimar Allah.

Gabatarwar Littafin Wakar Wakoki

An ce kaunar da ke tsakanin bashulammiyar da saurayinta mai kiwo na kamar “harshen wuta” na Jah. Me ya sa?

Gabatarwar Littafin Ishaya

Littafin Ishaya na dauke da annabcin da babu kuskure a cikinsa da zai iya karfafa ka cewa Jehobah mai cika alkawuransa ne.

Gabatarwar Littafin Irmiya

Irmiya ya ci gaba da yin hidimarsa a matsayin annabi duk da wahalar da ya sha. Ka yi tunani a kan darassin da za mu iya koya daga misalinsa.

Gabatarwar Littafin Makoki

Annabi Irmiya ne ya rubuta littafin Makoki, a littafin an yi makoki don yadda aka halaka Urushalima da kuma yadda yin tuba ke sa Allah ya jikanmu.

Gabatarwar Littafin Ezekiyel

Cikin saukin kai da kuma karfin zuciya, Ezekiyel ya yi duk aikin da Jehobah ya ba sa komin wuyarsa. Za mu iya amfana daga misalinsa a yau.

Gabatarwar Littafin Daniyel

Daniyel da abokansa sun rike amincinsu ga Jehobah duk da abin da suka fuskanta. Za mu iya amfana daga misalinsu da kuma yadda annabci suka cika.

Gabatarwar Littafin Hosiya

Annabcin Hosiya na dauke da darussa masu muhimmanci game da jin kan Jehobah ga masu zunubi da suka tuba da kuma irin ibadar da yake so mu yi masa.

Gabatarwar Littafin Joel

Annabi Joel ya yi annabci a kan babbar ranar Jehobah kuma ya bayyana abubuwan da za su sa mutum ya tsira. Annabcin da ya yi yana da muhimmanci a yau.

Gabatarwar Littafin Amos

Jehobah ya yi amfani da wannan mutumi mai tawali’u don ya yi aiki mai muhimmanci. Wadanne darussa ne za mu koya daga annabi Amos?

Gabatarwar Littafin Obadiya

Littafin Obadiya shi ne littafin da ba shi da yawa a cikin dukan littattafan Ibraniyawa ko kuma Tsohon Alkawari. Littafin na dauke da bayanan da za su karfafa mu da kuma alkawarin cewa za a daukaka sarautar Jehobah.

Gabatarwar Littafin Yunana

Annabin ya karbi gyara da aka yi masa, ya yi aikin da aka ba shi, kuma ya koyi darasi daga yadda Jehobah yake nuna kauna da jin kai. Za ka iya koyan darussa daga labarinsa.

Gabatarwar Littafin Mikah

Wannan annabcin zai sa mu kara kasance da tabbaci cewa Jehobah yana sa mu yi abubuwan da za su amfane mu.

Gabatarwar Littafin Nahum

Annabcin ya sa mu kasance da tabbaci cewa Jehobah yana cika alkawarinsa a koyaushe kuma yana taimaka wa dukan wadanda suka dogara ga sarautarsa.

Gabatarwar Littafin Habakkuk

Mu gaskata cewa Jehobah ya san lokaci da kuma hanyar da zai bi ya ceci mutanensa.

Gabatarwar Littafin Zafaniya

Me ya sa ya kamata mu guji yin tunani cewa ranar hukuncin Jehobah ba za ta zo ba?

Gabatarwar Littafin Haggai

Annabcin da ya nuna amfanin daukar ibadarmu ga Allah da muhimmanci fiye da abubuwan da muke so.

Gabatarwar Littafin Zakariya

Wahayi da annabci da yawa sun karfafa mutanen Allah a dā sosai. A yau ma, wadannan annabce-annabcen suna karfafa mu cewa Jehobah yana tare da mu.

Gabatarwar Littafin Malakai

Annabci ne game da ka’idodin Jehobah marar canjawa da jin kansa da kuma kauna. Annabcin yana kuma dauke da darussa za su iya taimaka mana a zamaninmu.

Gabatarwar Littafin Matta

Ka ji daɗin bincika abubuwa masu muhimmanci game da wannan littafin wanda shi ne na farko cikin Linjila huɗu.

Gabatarwar Littafin Markus

Littafi mafi gajerta a cikin littattafan bishara, ya ba da bayani a kan sarautar da Yesu zai yi a nan gaba a Mulkin Allah.

Gabatarwar Littafin Luka

Wadanne bayanai ne ke littafin Luka da sauran littattafan Bishara ba su da shi?

Gabatarwar Littafin Yohanna

Littafin Yohanna ya bayyana kaunar da Yesu yake wa ’yan adam da yadda ya kasance da saukin kai da kuma yadda ya nuna cewa shi ne Almasihu, Sarkin Mulkin Allah.

Gabatarwar Littafin Ayyukan Manzanni

Kiristoci a karni na farko sun yi kokari sosai wajen yada bishara ga mutane a fadin duniya. Labarin da ke littafin Ayyukan Manzanni zai sa ka kara kwazo a wa’azi.

Gabatarwar Littafin Romawa

Umurni game da halin rashin son kai na Allah da kuma muhimmancin gaskatawa da Yesu.

Gabatarwar Littafin 1 Korintiyawa

Wasikar manzo Bulus ta kunshi gargadi game da hadin kai da halaye masu kyau da kauna da kuma tashin matattu.

Gabatarwar Littafin 2 Korintiyawa

Jehobah, “Allah wanda yake yi mana kowace irin ta’aziyya” yana karfafa da kuma taimaka wa bayinsa.

Gabatarwar Littafin Galatiyawa

Wasikar da Bulus ya rubuta wa Galatiyawa yana da amfani a gare mu a yau kamar yadda ya amfani Kiristoci a lokacin. Za ta taimaka wa dukan Kiristoci su rike amincinsu.

Gabatarwar Littafin Afisawa

Wannan hurariyar wasikar ta nuna yadda Allah zai kawo salama da hadin kai ta wurin Yesu Kristi.

Gabatarwar Littafin Filibiyawa

Idan muka kasance da aminci duk da tsanantawa, hakan zai karfafa wasu su kasance da aminci.

Gabatarwar Littafin Kolosiyawa

Za mu faranta ran Jehobah idan muka yi amfani da abin da muke koya, muka gafarta wa ’yan’uwa kuma muka fahimci matsayin Yesu da ikonsa.

Gabatarwar Littafin 1 Tasalonikawa

Muna bukata mu kasance a fadake a ibada, ‘mu gwada kome,’ ‘mu yi ta yin addu’a babu fasawa,’ mu kuma karfafa juna.

Gabatarwar Littafin 2 Tasalonikawa

Bulus ya gyara ra’ayin da bai dace ba game da zuwan ranar Jehobah, kuma ya karfafa ’yan’uwa su tsaya da karfi a bangaskiyarsu.

Gabatarwar Littafin 1 Timoti

Bulus ya rubuta 1 Timoti don ya ba da wasu umurni da ikilisiyar za ta rika bi da kuma ja kunnen ’yan’uwa game da koyarwar karya da son kudi.

Gabatarwar Littafin 2 Timoti

Bulus ya karfafa Timoti ya yi hidimar da aka ba shi da kyau.

Gabatarwar Littafin Titus

Wasikar Bulus ta magance wasu matsaloli da ake fuskanta a ikilisiyar Kirit kuma ta nuna halayen da ’yan’uwa maza za su nuna domin su cancanci zama dattawa a ikilisiya.

Gabatarwar Littafin Filimon

Wannan gajeriyar wasikar ta kunshi halaye masu amfani kamar su tawali’u da alheri da kuma gafartawa.

Gabatarwar Littafin Ibraniyawa

Ba haikali ko kuma hadayar dabbobi ne tushen imanin Kiristoci ba, amma wani abu ne da ya fi hakan.

Gabatarwar Littafin Yakub

Yakub ya yi amfani da kalmomi wajen koyar da muhimman ka’idodin Littafi Mai Tsarki.

Gabatarwar Littafin 1 Bitrus

Wasikar Bitrus na biyu ta karfafa mu mu kasance da kwazo kuma mu danka ma Allah dukan damuwoyinmu.

Gabatarwar Littafin 2 Bitrus

Wasikar Bitrus ta biyu ta karfafa mu mu rike amincinmu yayin da muke jiran sabuwar sammai da sabuwar duniya.

Gabatarwar Littafin 1 Yohanna

Wasikar Yohanna ta gargade mu mu guji magabcin Almasihu kuma ta taimaka mana mu san abubuwan da ya kamata mu so da wadanda bai kamata mu so ba.

Gabatarwar Littafin 2 Yohanna

Wasikar Yohanna ta biyu ta tuna mana cewa mu ci gaba da tafiya cikin gaskiya kuma mu guje wa mayaudara.

Gabatarwar Littafin 3 Yohanna

Wasikar Yohanna ya koya mana muhimmancin karban baki a matsayinmu na Kiristoci.

Gabatarwar Littafin Yahuda

Yahuda ya fallasa da kuma bayyana dabarun da wasu ke amfani da su don su rudi Kiristoci.

Gabatarwar Littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna

Ka ga yadda wahayin da aka nuna wa Yohanna ya kwatanta yadda Mulkin Allah zai cika nufin Allah ga duniya da ma ’yan Adam.

Mai Yiwuwa Za Ka Kuma So