Sunayen Su Waye ne ke Rubuce Cikin “Littafin Rai”
Amsar Littafi Mai Tsarki
“Littafin rai,” da ake kira “littafin tunawa,” yana dauke da sunayen mutanen da za su sami rai na har abada. (Ru’ya ta Yohanna 3:5; 20:12; Malakai 3:16) Allah yana zaban sunayen nan dangane da yadda mutumin ya kasance da aminci a gare shi ne.—Yohanna 3:16; 1 Yohanna 5:3.
Allah yana tune da kowanne bawansa da ya kasance da aminci, kamar yana rubuta sunayensu ne cikin wani littafi, tun “kahuwar duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 17:8) Mutum na farko mai aminci da sunansa ke cikin littafin rai shi ne Habila. (Ibraniyawa 11:4) Littafin rai, ba kawai yana dauke da sunayen masu aminci ba, amma yana nuna mana cewa Jehobah Allah ne mai kauna wanda “ya san wadanda ke nasa.”—2 Timotawus 2:19; 1 Yohanna 4:8.
Shin za a iya share sunaye daga “littafin rai”?
Hakika. Ga abin da Allah ya ce wa masu rashin biyayya a Isra’ila ta dā: “Wanda ya yi zunubi gareni duka, shi ne zan shafe daga cikin littafina.” (Fitowa 32:33) Amma idan muka kasance da aminci za a bar sunayenmu cikin “littafin rai.”—Ru’ya ta Yohanna 20:12.