Me Ake Nufi da Cewa “Ku Kaunaci Masu Gāba Da Ku”?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Saꞌad da Yesu yake ba da huduba a kan dutse, ya ce: “ku kaunaci masu gāba da ku.” (Matiyu 5:44; Luka 6:27, 35) Abin da ya fada ya nuna cewa ya kamata mu kaunaci wadanda suka tsane mu ko kuma suka wulakanta mu.
Yesu ya nuna cewa yana kaunar abokan gābansa ta wajen gafarta wa wadanda suka wulakanta shi. (Luka 23:33, 34) Abin da ya fada ya jitu da abin da ke nassosin Ibrananci, wato Littattafan da ake kira tsohon alkawari.—Fitowa 23:4, 5; Karin Magana 24:17; 25:21.
“Ku kaunaci wadanda ba sa kaunar ku, ku yi wa masu tsananta muku adduꞌa.”—Matiyu 5:43, 44.’
A talifin nan za ka ga
Dalilin da ya sa za ka kaunaci abokan gābanka
Allah ya nuna misali mai kyau. Allah “mai alheri ne ga mutanen da ba sa godiya da kuma mugaye.” (Luka 6:35) Yana “sa rana ta yi haske a kan . . . marasa kirki ma.” (Matiyu 5:45)
Kauna za ta iya sa abokin gābanka ya canja halinsa. Littafi Mai Tsarki ya ce mu rika yi wa abokan gābanmu alheri, kuma ya ce idan muka yi hakan, muna “jibga garwashin wuta a kansa.” (Karin Magana 25:22) Kwatancin da aka yi yana nufin yadda ake kona wani irin dutse kuma ya narke don a sami duwatsu masu daraja. Hakazalika, idan muka nuna wa wanda ya tsane mu alheri, kamar mun narkar da fushinsa ne kuma muka sa ya nuna halin kirki.
Ta yaya za ka kaunaci abokan gābanka?
“Ku yi wa wadanda ba sa son ganinku alheri.” (Luka 6:27) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan abokin gābanka yana jin yunwa, sai ka ba shi abinci. Idan yana jin kishin ruwa, sai ka ba shi ruwan sha.” (Romawa 12:20) Za ka sami wasu hanyoyin da za ka iya nuna wa abokan gābanka kauna ta wajen bin shawarar da Yesu ya bayar cewa: “Ku yi wa mutane abin da kuke so su yi muku.”—Luka 6:31.
“Ku sa wa masu zaginku albarka.” (Luka 6:28) Za mu iya sa wa abokan gābanmu albarka ta wajen yi musu magana da kyau kuma cikin kwanciyar hankali, ko da suna zagin mu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku rama . . . zagi da zagi. Ku rama dai da albarka.” (1 Bitrus 3:9) Bin shawarar nan za ta taimaka mana mu dakatar da kiyayya
“Ku kuma yi wa masu ba ku wahala adduꞌa.” (Luka 6:28) Idan wani ya zage ka ko ya wulakanta ka, kada ka “saka masa da mugunta.” (Romawa 12:17) A maimakon haka, ka roki Allah ya gafarce mutumin. (Luka 23:34; Ayyukan Manzanni 7:59, 60) Maimakon ka rama abin da mutumin ya yi maka, ka bar ma Allah ya saka masa bisa ga adalcinsa.—Littafin Firistoci 19:18; Romawa 12:19.
“Ku kaunaci masu gāba da ku, ku yi wa wadanda ba sa son ganinku alheri. Ku sa wa masu zaginku albarka, ku kuma yi wa masu ba ku wahala adduꞌa.” —Luka 6:27, 28.
Ka zama mai “hakuri da kirki.” (1 Korintiyawa 13:4) Saꞌad da manzo Bulus yake kwatanta yadda kauna take, ya yi amfani da kalmar Helenancin nan (a·gaʹpe) kuma kalmar nan ne aka yi amfani da ita a Matiyu 5:44 da Luka 6:27, 35. Muna nuna irin kaunar nan ga kowa har da abokan gābanmu ta wajen zama mai hakuri da kirki, ba mai kishi ko girman kai ko mai wulakanta mutane ba.
“Kauna tana da hakuri da kirki, kauna ba ta jin kishi, ba ta yin takama, ba ta yin girman kai, ba ta yin daga kai, ba ta kin kula da yadda wadansu za su ji, ba ta sonkai, ba ta jin tsokana, ba ta rike laifi a zuciya. Kauna ba ta jin dadin mugunta, amma takan ji dadin gaskiya. Kauna takan sa hakuri cikin kowane hali, da bangaskiya cikin kowane hali, da sa zuciya cikin kowane hali, da kuma jimiri cikin kowane hali. Kauna ba ta kārewa har abada.”—1 Korintiyawa 13:4-8.
Zai dace ka yi yaki da abokan gābanka ne?
Aꞌa, bai kamata ba, Yesu ya koya wa mabiyansa cewa kada su yi fada da abokan gābansu. Alal misali, lokacin da ya gargadi mabiyansa game da yadda za a kawo wa Urushalima hari, bai gaya musu cewa su yi fada ba, amma ya ce su gudu su bar garin. (Luka 21:20, 21) Yesu ya kuma gaya wa Bitrus cewa: “Mai da takobinka, gama duk wanda ya dauki takobi, takobi ne zai kashe shi.” (Matiyu 26:52) Littafi Mai Tsarki da kuma tarihi sun nuna cewa mabiyan Yesu na karni na farko ba su yi yaki da abokan gābansu ba. a—2 Timoti 2:24.
Karya game da kaunar abokan gāba
Karya: A cikin Dokar Allah an umurci Israꞌilawa su tsane abokan gābansu.
Gaskiya: Babu irin Dokar nan a Dokokin da Allah ya ba su. Maimakon haka, an ce wa Israꞌilawan su kaunaci makwabtansu. (Littafin Firistoci 19:18) Ko da yake kalmar nan “makwabci” yana nufin dukan mutane. Amma wasu Yahudawa suna cewa makwabtansu Yahudawa ne kamar su, kuma suna ganin cewa ya kamata su tsane wadanda ba Yahudawa ba don abokan gābansu ne. (Matiyu 5:43, 44) Yesu ya daidaita raꞌayinsu ta wajen ba su wani labari game da wani mutumin Samariya.—Luka 10:29-37.
Karya: Kaunar abokan gāba yana nufin amincewa da halayensu marasa kyau.
Gaskiya: Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa za ka iya kaunar mutum ba tare da ka amince da halayensa marar kyau ba. Alal misali, Yesu ya tsane mugunta amma ya yi adduꞌa a madadin wadanda suka kashe shi. (Luka 10:29-37) Ya tsani rashin bin doka ko zunubi, amma ya ba da ransa don ya fanshe masu zunubi.—Yohanna 3:16; Romawa 6:23.
a Littafin The Rise of Christianity wanda E. W. Barnes ya rubuta ya ce: “Daga binciken da aka yi, an gano cewa, har lokacin da Marcus Aurelius [Shugaban Romowa da ya yi mulki daga 161 zuwa 180 kafin haihuwar Yesu], babu wani Kirista da ya zama soja, ko kuma babu wani soja da ya ci gaba da aikin soja bayan da ya zama Kirista.”