Shin Mulkin Allah a Zuciyarka Yake?
Amsar Littafi Mai Tsarki
A’a, Mulkin Allah ba wani yanayi ba ne da ke zuciyar Kiristoci. a Littafi Mai Tsarki ya gaya mana inda mulkin yake ta wajen kiransa “mulkin sama.” (Matiyu 4:17) Ka ga yadda Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mulkin gwamnati ce da take sarauta a sama.
Mulkin Allah yana da masu sarauta da talakawa da dokoki da kuma wani mai iko da zai sa a rika yin nufin Allah a sama da kuma duniya.—Matiyu 6:10; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 5:10.
Mulkin Allah ko kuma gwamnatin Allah zai yi sarauta a kan dukan “kabilu, da al’ummai, da yare dabam-dabam” da ke nan duniya. (Daniyel 7:13, 14) Wanda zai yi sarauta zai yi amfani da ikon da Allah ya ba shi ba wanda talakawan mulkinsa suka ba shi ba.—Zabura 2:4-6; Ishaya 9:7.
Yesu ya gaya wa manzanninsa masu aminci cewa za su kasance tare da shi a Mulkin sama kuma su zauna a “kujerun mulki.”—Luka 22:28, 30.
Mulkin zai hallaka magabtansa.—Zabura 2:1, 2, 8, 9; 110:1, 2; 1 Korintiyawa 15:25, 26.
Littafi Mai Tsarki bai koyar cewa Mulkin Allah yana zukatan mutane kuma yana mulki a zukatansu ba. Amma ya nuna cewa “kalmar mulkin” ko kuma “labari mai dadi na mulkin” zai iya shafan zukatan mutane.—Matiyu 13:19; 24:14.
Mene ne furucin nan “mulkin Allah yana nan a cikinku” yake nufi?
Yadda wasu juyin Littafi Mai Tsarki suka fassara Luka 17:21 ya sa wasu mutane sun rikice game da inda Mulkin Allah yake. Alal misali, Littafi Mai Tsarki Cikin Tsohuwar Hausa A Saukake ya ce “mulkin Allah yana cikinku.” Don mu fahimci wannan ayar da kyau, muna bukatar mu san su waye ne Yesu yake magana da su.
Yesu yana magana ne da Farisiyawa, wato malaman addinai wadanda suke adawa da shi kuma suka kulla a kashe shi. (Matiyu 12:14; Luka 17:20) Shin kana ganin Mulkin Allah wani abu ne da ke zuciyarsu mai cike da mugunta? Yesu ya gaya musu cewa: “Cike kuke da munafunci da mugayen ayyuka.”—Matiyu 23:27, 28.
Wasu juyin Littafi Mai Tsarki sun fassara Luka 17:21 daidai yadda za a fahimta. Daya daga cikinsu ya ce: ‘Mulkin Allah a tsakaninku yake.’ (Littafi Mai Tsarki) Wani juyin kuma ya ce: “Mulkin Allah yana nan tare da ku.” (New World Translation, karin bayani) Mulkin Allah yana a tsakanin Farisiyawan ko kuma tare da Farisiyawan domin Yesu wanda shi ne Sarkin Mulkin Allah yana tsaye a gabansu a wurin.—Luka 1:32, 33.
a Coci da yawa suna koyarwa cewa Mulkin Allah wani abu ne da ke cikin zuciyar mutum. Alal misali, wani coci mai suna Southern Baptist Convention a Amirka ya ce Mulkin Allah shi ne “yadda Allah yake mulki a zuciyar mutum da kuma rayuwarsa gabaki daya.” Hakazalika a littafin nan Jesus of Nazareth da Pope Benedict XVI ya rubuta ya ce, “mutum yakan zama da Mulkin Allah a zuciyarsa idan yana biyayya ga Allah.”