Shin Iblis Yana Wanzuwa da Gaske?
Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da
Hakika, Iblis yana wanzuwa. Shi ne “sarkin duniya,” kuma shi ruhu ne da ya zama mugu da ya yi wa Allah tawaye. (Yohanna 14:30; Afisawa 6:11, 12) Littafi Mai Tsarki ya kwatanta halayen Iblis da wadannan sunaye:
Shaidan, wanda ke nufin “Magabci.”—Ayuba 1:6.
Iblis, wanda ke nufin “Mai tsegumi.”—Ru’ya ta Yohanna 12:9.
Maciji, wanda a wasu lokatai ana amfani da shi a Littafi Mai Tsarki a matsayin “Mayaudari.”—2 Korintiyawa 11:3.
Mai-jaraba.—Matta 4:3.
Makaryaci.—Yohanna 8:44.
Iblis ba ya nufin mugun tunani ko hali da muke da shi
Wasu sun dauka cewa Shaidan Iblis wani mugun tunani ne ko kuma hali da muke da shi. Amma, an rubuta wata tattaunawa da Jehobah da Shaidan suka yi cikin Littafi Mai Tsarki. Allah mai tsarki ne, don haka, ba wai hira yake yi da wani mugun tunanin da ke cikinsa ba. (Kubawar Shari’a 32:4; Ayuba 2:1-6) Hakanan ma, Shaidan ya gwada Yesu wanda shi ma marar aibi ne. (Matta 4:8-10; 1 Yohanna 3:5) Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Iblis wani ne mai rai, shi ba wani mugun tunani ko halin da ke cikinmu ba ne.
Da yake mutane da yawa ba su gaskata da wanzuwar Iblis ba, ya kamata hakan ya ba mu mamaki ne? Ko kadan, domin Littafi Mai Tsarki ya ce Shaidan yana amfani da rudu don ya cim ma burinsa. (2 Tasalonikawa 2:9, 10) Hanya daya da yake yin hakan ita ce ta wurin sa mutane su gaskata cewa ba ya wanzuwa.—2 Korintiyawa 4:4.
Wasu ra’ayoyin karya game da Iblis
Kāge: Lucifer wani sunan Iblis ne.
Gaskiyar: Kalmar Hellenanci da wasu Littafi Mai Tsarki suka fassara zuwa “Lucifer” yana nufin “mai haske.” (Ishaya 14:12, Littafi Mai Tsarki) Mahallin littafin ya nuna cewa wannan kalmar tana nufin zuriyar sarakunan Babila, da Allah zai halaka saboda fahariyarta. (Ishaya 14:4, 13-20) An yi amfani da furucin nan “mai haske” don a kushe sarakunan Babila bayan da aka halaka birnin.
Kāge: Allah yana amfani da shaidan a matsayin “mai hukunci.”
Gaskiyar: Iblis magabcin Allah ne, ba bawansa ba. Shaidan Iblis yana adawa da wadanda suke bauta wa Allah kuma yana zarginsu.—1 Bitrus 5:8; Ru’ya ta Yohanna 12:10.