Sunaye Nawa Ne Allah Yake da Su?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Suna daya ne kawai Allah yake da shi. Wadannan su ne harufan יהוה a Ibrananci amma a Turanci sunan “Jehovah” ne. a Allah ya hure annabi Ishaya ya rubuta cewa: “Ni ne Jehobah; wannan ne sunana.” (Isha. 42:8, New World Translation) Sunan Allah Jehobah ya bayyana a Littafi Mai Tsarki na dā kusan sau 7,000 kuma an fi amfani da sunan fiye da kowane lakabi, ban da haka ma, ya fi kowace suna da aka yi amfani da shi yawa. b
Shin Allah yana da wasu sunaye Ne?
Ko da yake Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da suna daya kawai, ya yi amfani da wasu lakabi don ya kwatanta shi. Jerin da ke kasa ya nuna wadannan lakabi da kwatancin da suka nuna yadda Jehobah yake da kuma halinsa.
Lakabi |
Kwatanci |
Ma’ana |
---|---|---|
Mai-Iko Duka |
Farawa 17:1 |
Yana da iko sosai. An ambata wannan kalmar Ibrananci ʼEl Shad·daiʹ wato Allah Mai Iko Duka sau bakwai a cikin Littafi Mai Tsarki. |
Alpha da Omega |
Ru’ya ta Yohanna 1:8; 21:6; 22:13 |
“Na fari da na baya” ko kuma “farko da ƙarshe,” suna nufin babu wani Allah Mai-Iko Duka kafin Jehobah kuma babu wani bayansa. (Ishaya 43:10) Alpha da Omega su ne haruffa na farko da kuma na ƙarshe a Girkanci. |
Mai-Zamanin Dā |
Daniyel 7:9, 13, 22 |
Ba shi da farko kuma zai kasance har abada fiye da duk wani abu ko halitta.—Zabura 90:2. |
Mahalicci |
Ishaya 40:28 |
Shi ya halicci kome. |
Uba |
Matta 6:9 |
Shi ya ba da rai. |
Allah |
Farawa 1:1 |
Mai-iko wanda ya cancanci a bauta masa. Wannan kalmar Ibrananci ʼElo·him,ʹ jam’i ce kuma tana nufin cewa Jehobah mai iko ne ko mai girma. |
Allahn alloli |
Kubawar Shari’a 10:17 |
Allah na gaske wanda ya bambanta da “gumaka” da wasu ke bauta wa.—Ishaya 2:8. |
Mai-koya mana |
Ishaya 30:20, 21 |
Yana koyarwa kuma ya ba da umurni a hanyar da za mu amfana.—Ishaya 48:17, 18. |
Mahalicci |
Zabura 149:2 |
Shi ya halicci kome.—Ru’ya ta Yohanna 4:11. |
Allah Mai-Farin Ciki |
1 Timotawus 1:11 |
Allah mai farin ciki.—Zabura 104:31. |
Mai-jin addu’a |
Zabura 65:2 |
Yana jin addu’o’in bayinsa masu aminci. |
Ina Yadda Nike |
Fitowa 3:14, King James Version |
Yana iya zama duk abin da zai zama don ya cika nufinsa. An fassara wannan Kalmar “Ina Yadda Nike” zuwa “Zan Zama Duk Abin da Nake So In Zama” ko “Zan Zama Duk Abin da Na ga Dama.” (The Emphasised Bible, by J. B. Rotherham; New World Translation) Hakan ya taimaka wajen fahimtar sunan Allah, Jehobah, da ke cikin aya ta gaba.—Fitowa 3:15. |
Mai kishi |
Fitowa 34:14, King James Version |
Yana so mutane su bauta masa shi kadai. An fassara wannan Kalmar zuwa “wanda ba ya so a bauta wani Allah baicinsa.”—God’s Word Bible; New World Translation. |
Sarkin zamanai |
Ru’ya ta Yohanna 15:3 |
Sarautarsa ba ta da farko ko karshe. |
Ubangiji |
Zabura 135:5 |
Mai shi ko shugaba; A Ibrananci ʼA·dhohnʹ da ʼAdho·nimʹ. |
Ubangiji mai-runduna, Ubangijin Assabbaci |
Ishaya 1:9; King James Version; Romawa 9:29, King James Version |
Shugaban dukan mala’iku. Wannan Kalmar “Ubangijin Assabbaci” tana nufin “Jehobah mai-runduna” da kuma “Ubangijin rundunan sama.”—Romawa 9:29, New World Translation; NET Bible, karin bayani. |
Ubangiji Madaukaki |
Zabura 47:2 |
A duk sama da kasa, shi ne ya fi daukaka. |
Mafi-Tsarki |
Misalai 9:10 |
Shi ne mafi tsarki. |
Maginin Tukwane |
Ishaya 64:8 |
Kamar yadda mai yin tukwane yake da iko a kan yumbu, haka ma Jehobah yake da iko a kan mutanen da kuma al’ummai.—Romawa 9:20, 21. |
Mai-Fansarka |
Ishaya 41:14, King James Version |
Shi ne ya ceto mu daga zunubi ta hanyar fansa da dansa Yesu Kristi ya ba da.—Yohanna 3:16. |
Dutse ko Fa |
Zabura 18:2, 46 |
Shi ne mai cetonmu kuma yana tsare mu. |
Mai-Ceto |
Ishaya 45:21 |
Shi ke cetonmu daga hatsari ko halaka. |
Makiyayi |
Zabura 23:1 |
Yana kula da bayinsa. |
Ubangiji Yahweh |
Farawa 15:2 |
Yana da ikon da ba irinsa; Ibrananci ʼAdho·naiʹ. |
Madaukaki |
Daniyel 7:18, 27 |
Madaukaki mafi girma. |
Sunayen da aka yi amfani da su a Nassosin Ibrananci
An yi amfani da sunan Allah a cikin Littafi Mai Tsarki, amma ba a sauya sunan da wasu lakabi ba.
Sunayen da aka yi amfani da su |
Kwatanci |
Ma’ana |
---|---|---|
Jehobah-jireh |
Farawa 22:13, 14 |
“Jehobah Zai Tanadar.” |
Yahweh-nissi |
Fitowa 17:15 |
“Jehobah Shi Ne Abin Jingina.” (Today’s New International Version) Jehobah shi ne Allahn da mutane suke dogara a kansa.—Fitowa 17:13-16. |
Jehobah-shalom |
Alkalawa 6:23, 24 |
“Jehobah salama ne.” |
Yahweh-shammah |
Ezekiyel 48:35 |
“Ubangiji yana nan wurin.” |
Dalilai da suka sa ya kamata mu san sunan Allah kuma mu yi amfani da shi
Allah ya san cewa sunan shi Jehobah na da muhimmanci sosai, shi ya sa ya saka sunan a cikin Littafi Mai Tsarki so dubbai.—Malakai 1:11.
Ɗan Allah, Yesu ya nuna muhimmancin sunan Allah. Alal misali, ya yi addu’a ga Jehobah, ya ce: “A tsarkake sunanka.”—Matta 6:9; Yohanna 17:6.
Mutane suna kusantar Jehobah sa’ad da suka soma sanin sunan Allah kuma suka fara amfani da shi. (Zabura 9:10; Malakai 3:16) Za su amfana daga alkawuran Allah idan suka kulla dangantaka da Allah: ‘Tun da ya kallafa kaunarsa a gareni, domin wannan zan tsamar da shi, zan ɗaukaka shi, domin ya san sunana.’—Zabura 91:14.
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gama ko da yake akwai waɗanda ake ce da su alloli, ko a sama ko a duniya; akwai fa alloli da yawa, iyayengiji kuma da yawa haka.” (1 Korintiyawa 8:5, 6) Kari ga haka, ya nuna cewa Allah sunansa ne Jehobah.—Zabura 83:18.
a Wasu masana Ibraniyawa sun fi son a fassara sunan nan Allah zuwa “Yahweh.”
b An gajarta sunan Jehobah zuwa Jah kuma hakan ya bayyana wajen sau 50 a Littafi Mai Tsarki, kari ga haka, muna iya jin sa a kalma nan “Hallelujah,” ko “Alleluia” da yake nufin “A Yabi Jah.”—Ru’ya ta Yohanna 19:1; American Standard Version; King James Version.