Yaushe ne Aka Haifi Yesu?
Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba
Littafi Mai Tsarki bai nuna kwanan watan da aka haifi Yesu Kristi ba, kamar yadda bincike na gaba ya nuna:
““Ba a san ainihin kwanan watan da aka haifi Kristi ba.”—New Catholic Encyclopedia.
““Ba a san ainihin ranar da aka haifi Kristi ba.”—Encyclopedia of Early Christianity.
Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai amsa tambayar nan, ‘Yaushe ne aka haifi Yesu?’ kai tsaye ba, amma ya bayana abubuwa biyu da suka auku a lokacin haihuwarsa da ya sa mutane da yawa suka san cewa ba a haife shi a 25 ga Disamba ba.
Ba a lokacin sanyi ba ne
Lokacin Kidayar mutane. Kafin a haifi Yesu, Kaisar Augustus ya ba da doka cewa “a rubuta [adadin] dukan mazaunan duniya.” Wannan yana bukatar kowa shi rubuta suna a “nasa birni,” hakan kuma yana bukatar doguwar tafiya na mako daya ko ma fiye da hakan. (Luka 2:1-3) Watakila wannan dokar—don ta taimaka wajen biyan haraji da kuma tilasta wa mutane su shiga aikin soja ne—saboda yin hakan a wani lokaci dabam zai yi wuya. Kari ga haka, zai yi wuya a ce Augustus ya tilasta wa mutanensa su yi irin wannan doguwar tafiya a lokacin sanyi.
Tumaki. Makiyaya suna “kwana a filin Allah, suna tsaron garken tumakinsu da dad dare.” (Luka 2:8, Littafi Mai Tsarki) Littafin nan Daily Life in the Time of Jesus ya lura cewa a waje ne tumaki suke kwanciya daga “mako kafin Idin Ketarewa [a karshen watan Maris]” zuwa tsakiyar watan Nuwamba. Ya kuma ce: “Sukan fake domin yawan sanyi; saboda haka, mun ga cewa kwanan watan da ake Kirsimati, a lokacin sanyi ba zai kasance daidai ba, tun da Lingila ta nuna cewa makiyaya suna waje a daren.”
A lokacin da aka fara kaka
Za mu iya sanin lokacin da aka haifi Yesu ta wurin kirga daga lokacin mutuwarsa a Idin Ketarewa na 14 ga watan Nisan a lokaci bazara a shekara ta 33 A Zamaninmu. (Yohanna 19:14-16) Yesu yana da shekara 30 lokacin da ya soma hidimarsa ta shekara uku da rabi, saboda haka, an haife shi ne a farkon kaka na shekara ta 2 kafin zamaninmu.—Luka 3:23.
Me ya sa ake Kirsimati a ranar 25 ga Disamba?
Tun da shi ke ba a haifi Yesu a ranar 25 ga Disamba ba, to me ya sa ake bikin Kirsimati a wannan ranar? Encyclopædia Britannica ya ce watakila limaman coci sun zabi ranar “don ya yi daidai da bikin arna na Romawa da suke ‘bikin haihuwar rana,’” da zai kori sanyi. Bisa ga The Encyclopedia Americana, dalibai da yawa sun gaskata cewa an yi haka ne “domin arna da suka tuba su so addinin Kirista.”