Yesu Ya Mutu Akan Gicciye Ne?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Mutane da yawa suna daukan gicciye cewa alama ce ta Kiristanci. Amma, Littafi Mai Tsarki bai kwatanta abin da Yesu ya mutu a kansa ba, saboda haka babu wanda zai san ainihin kamaninsa. Duk da, Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu ya mutu akan mikakken itace ba gicciye ba.
Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmar Helenancin nan ne stau·rosʹ sa’ad da yake zancen abin da aka kashe Yesu bisansa. (Matta 27:40; Yohanna 19:17) Ko da yake sau da yawa ana amfani da kalmar nan “gicciye” ne cikin fassara, dalibai sun ce yana nufin “mikakken gungume” ne. a A Critical Lexicon and Concordance to the English and Greek New Testament ya ce: Stau·rosʹ “ba ta nufin itace biyu da aka dora a kan juna ba.”
Littafi Mai Tsarki ma ya yi amfani da kalmar Helenancin nan xyʹlon makamancin stau·rosʹ. (Ayyukan Manzanni 5:30; 1 Bitrus 2:24) Kalmar nan tana nufin “itace,” “katako,” “gungume,” ko kuma “bishiya.” b The Companion Bible ya ya ce: “Babu wani abu cikin Helenanci na Sabon Alkawari da ke nuna cewa katakai biyu ba ne.”
Allah ya yarda a yi masa sujjada ta wurin yin amfani da gicciye ne?
Ko da akan me Yesu ya mutu, furuci da kuma ayoyin Littafi Mai Tsarki na gaban nan sun bayyana mana cewa kada mu yi amfani da gicciye a sujjadarmu ga Allah ba.
Allah ba ya yarda da sujjada da ake yi ta wurin yin amfani da sifoffi, alamu, har ma da gicciye ba. Allah ya umurci Isra’ilawa kada su yi amfani da “kama ba ko kadan” a sujjadarsu, haka ma aka ce wa Kiristoci su “guje ma bautar gumaka.”—Kubawar Shari’a 4:15-19; 1 Korintiyawa 10:14.
Kiristoci na farko ba su yi amfani gicciye a sujjadarsu ba. c Koyarwa da misalan manzanni tafarki ne da ya kamata dukan Kiristoci su bi.—2 Tasalinokawa 2:15.
Yin amfani da gicciye a sujjada ya fito ne daga wurin arna ne. d Shekaru da yawa bayan mutuwar Yesu, lokacin da cococi suka bijire daga koyarwarsa, aka kyalle sababbin mabiya su shigo da alamunsu na arna” da suka hada da gicciye. (The Expanded Vine’s Expository Dictionary of New Testament Words) Amma, Littafi Mai Tsarki ya haramta a bi al’adun arna wai don a sami masu tuba .—2 Korintiyawa 6:17.
a Dubi New Bible Dictionary, Juyi na Uku, da D. R. W. Wood ne editan, shafi na 245; Theological Dictionary of the New Testament, Kundi na VII, shafi na 572; The International Standard Bible Encyclopedia, Sabon Juyi, Kundi na 1, shafi 825; da kuma The Imperial Bible-Dictionary, Kundi na II, shafi na 84.
b Dubi The Expanded Vine’s Expository Dictionary of New Testament Words, shafi na 1165; A Greek-English Lexicon, na Liddell da Scott, Juyi na Tara, shafuffuka na 1191-1192; da Theological Dictionary of the New Testament, Kundi na V, shafi na 37.
c Dubi Encyclopædia Britannica, 2003, karkashin “Cross”; The Cross—Its History and Symbolism, shafi na 40; da The Companion Bible, Oxford University Press, rataye na 162, shafi na 186.
d Dubi The Encyclopedia of Religion, Kundi na 4, shafi na 165; The Encyclopedia Americana, Kundi na 8, shafi na 246; da Symbols Around Us, shafuffuka na 205-207.