Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 40

Dauda da Goliath

Dauda da Goliath

Jehobah ya gaya wa Sama’ila cewa: ‘Ka je gidan Jesse. Ɗaya daga cikin yaransa ne zai zama sarkin Isra’ila.’ Sai Sama’ila ya tafi gidan Jesse. Da ya gan ɗansa na fari, sai ya ce: ‘Babu shakka, wannan ne zai zama sarki.’ Amma Jehobah ya gaya wa Sama’ila cewa ba shi ba ne ya zaɓa. Jehobah ya ce: ‘Halin mutum nake gani ba jikinsa ba.’

Jesse ya ƙaro wa Sama’ila yaransa maza guda shida. Amma Sama’ila ya ce: ‘Babu wanda Jehobah ya zaɓa a cikinsu. Ba ka da wasu yaran kuma?’ Sai Jesse ya ce: ‘Akwai autansu mai suna Dauda. Ya je kiwon tumakina.’ Da Dauda ya zo, sai Jehobah ya gaya wa Sama’ila cewa: ‘Wannan ne!’ Sai Sama’ila ya zuba wa Dauda māi a kai kuma ya naɗa shi sarkin Isra’ila.

Bayan wani lokaci, sai Isra’ilawa suka je yin yaƙi da Filistiyawa. Waɗannan Filistiyawan suna da wani ƙaton soja, sunansa Goliath. Kowace rana, Goliath yana yi wa Isra’ilawa ba’a. Ya yi ihu kuma ya ce: ‘Ku turo wani mu yi faɗa. Idan ya yi nasara, za mu zama bayinku. Amma idan na yi nasara, za ku zama bayinmu.’

Da yake ’yan’uwan Dauda sojoji ne, sai Dauda ya je inda suke yaƙin don ya ba su abinci. Ya ji abin da Goliath ya faɗa, sai ya ce: ‘Zan yi faɗa da shi!’ Sarki Saul ya ce: ‘Kai ƙaramin yaro ne.’ Sai Dauda ya ce: ‘Jehobah zai taimaka mini.’

Saul ya ba Dauda kayan yaƙinsa amma Dauda ya ce: ‘Ba zan iya faɗa da waɗannan abubuwan ba.’ Dauda ya ɗauki majajjawarsa kuma ya je wani rafi. A wurin ya nemi duwatsu biyar kuma ya saka su a jakarsa. Sai Dauda ya je wurin Goliath a guje. Ƙaton ya ce da babbar murya: ‘Zo nan yaro. Zan ba da namanka ga tsuntsaye da kuma namomin daji.’ Dauda bai ji tsoro ba. Sai ya yi ihu kuma ya ce: ‘Ka zo wurina da doguwar wuƙa da kuma mashi, amma na zo da sunan Jehobah. Ba da mu kake faɗa ba amma da Allah kake yi. Kowa a nan zai ga cewa Jehobah ya fi doguwar wuƙa da mashi ƙarfi. Zai sa mu halaka dukan ku.’

Dauda ya saka dutse a cikin majajjawarsa kuma ya kaɗa ta da ƙarfi sosai. Da taimakon Jehobah, dutsen ya fita kuma ya sami Goliath a goshi. Sai ƙaton ya faɗi a ƙasa ya mutu. Filistiyawan da ke tare da shi suka gudu. Kana dogara ga Jehobah kamar Dauda kuwa?

“A wurin mutane ba shi yiwuwa, amma ga Allah ba haka ba ne: gama ga Allah abubuwa duka ya yiwu.”​—Markus 10:27