Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 3

Yadda Za Ku Warware Matsaloli

Yadda Za Ku Warware Matsaloli

“Ku himmantu ga ƙaunar juna gaya, domin ƙauna takan yafe laifofi masu ɗumbun yawa.”1 Bitrus 4:8, Littafi Mai Tsarki

Bayan aurenku, matsaloli dabam-dabam za su kunno kai. Waɗannan matsalolin suna iya tasowa a sakamakon bambancin ra’ayi da bambancin tunani da kuma yadda kuke tafiyar da rayuwa. Ƙari ga haka, matsaloli suna iya zuwa daga wurare dabam-dabam har da abubuwa na ba-zato.

Maimakon mu guje wa matsalolin da muke fuskanta, Littafi Mai Tsarki ya shawarce mu mu magance su. (Matta 5:23, 24) Idan kuka bi ka’idodin Littafi Mai Tsarki, hakan zai taimaka muku ku magance matsalolinku.

1 KU TATTAUNA MATSALAR

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Akwai lokacin . . . magana.” (Mai-Wa’azi 3:1, 7) Ku tabbata cewa kun tattauna matsalar sosai. Ka gaya wa matarka ainihin abin da ke zuciyarka da kuma ra’ayinka a kan batun. A kowane lokaci, ku gaya ‘wa junanku . . . gaskiya.’ (Afisawa 4:25) Ko da abin ɓacin rai ya faru, kada ku yi faɗa. Idan ka yi maganar da za ta sanyaya zuciyar matarka, ba za ku yi babban gardama ba.Misalai 15:4; 26:20.

Ko da ba ku jitu a kan wani batu ba, ku ci gaba da yi wa juna alheri. Kada ku manta cewa ya kamata ku riƙa nuna wa juna ƙauna da ban girma. (Kolosiyawa 4:6) Ku yi ƙoƙari ku sasanta matsalar da ke tsakaninku nan da nan, kuma kada ku ƙi yin magana da juna.—Afisawa 4:26.

SHAWARA:

  • Ku keɓe lokaci don tattauna matsalar da ke tsakaninku

  • Idan matarka tana magana, ka yi ƙoƙari ka ƙyale ta ta gama magana. Idan ta gama, sai ka yi magana

2 KU SAURARA KUMA KU FAHIMCI JUNA

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Ku ƙaunaci juna gaya. Wajen ba da girma, kowa ya riga ba ɗan’uwansa.” (Romawa 12:10, LMT) Yana da muhimmanci ka kasa kunne da kyau sa’ad da matarka take magana. Ka yi ƙoƙari ka fahimci ra’ayinta kuma ka yi hakan da ‘juyayi’ da kuma ‘tawali’u.’ (1 Bitrus 3:8; Yaƙub 1:19) Kada ka yi kamar kana saurara kawai. Idan da hali, ka bar abin da kake yi gabaki ɗaya don ka saurari matarka sosai, ko kuma ka tambaye ta ko za ku iya tattauna batun a wani lokaci. Idan kuka ɗauki juna a matsayin abokai maimakon ­abokan gāba, ba za ku yi ‘garajen  . . . yin fushi’ ba.Mai-Wa’azi 7:9.

SHAWARA:

  • Ko da abin da matarka take faɗa yana ci maka rai, ka ci gaba da saurarawa don ka fahimce ta

  • Ka mai da hankali ga abin da take nufi maimakon kalmomin da take furtawa. Ka lura da ­muryarta da kuma fuskarta ­yayin da take magana

3 KU YI DUK ABIN DA KUKA SHAWARTA

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “A cikin dukan aiki akwai riba: Amma taɗin baki ba ya nufa koina sai wajen tsiya.” (Misalai 14:23) Yanke shawara mai kyau kawai ba shi ne aikin ba. Kuna bukatar ku yi abin da kuka shawarta za ku yi. Yin hakan ba zai kasance da sauƙi ba, amma za ku sami sakamako mai kyau. (Misalai 10:4) Idan kuka ba juna haɗin kai, za ku girbi ‘amfanin wahalarku.’Mai-Wa’azi 4:9, LMT.

SHAWARA:

  • Kowannenku ya ƙudura yin abin da zai iya yi don ku warware matsalar da ke tsakaninku

  • A lokaci-lokaci, ku zauna ku ­bincika don ku ga ko kuna ­samun ci gaba a wannan batun