FARA MAGANA DA MUTANE
DARASI NA 6
Karfin Hali
Ƙaꞌida: ‘Mun yi ƙarfin hali cikin Allahnmu da za mu faɗa maku bisharar Allah.’—1 Tas. 2:2, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.
Abin da Yesu Ya Yi
1. Ka kalli BIDIYON, ko ka karanta Luka 19:1-7. Saꞌan nan ka yi tunani a kan tambayoyin nan:
Mene ne Abin da Yesu Ya Yi Ya Koya Mana?
2. Muna bukatar ƙarfin hali don mu iya yi wa kowa da kowa waꞌazi.
Ka Yi Koyi da Yesu
3. Ka dogara ga Jehobah. Ruhun Allah ne ya ba wa Yesu ƙarfin hali ya yi waꞌazi. Kai ma zai iya taimaka maka ka yi hakan. (Mat. 10:19, 20; Luk. 4:18) Ka roƙi Jehobah ya ba ka ƙarfin hali don ka yi waꞌazi ga mutanen da mai yiwuwa kake jin tsoron su.—A. M. 4:29.
4. Kada ka ɗauka cewa mutumin ba zai saurare ka ba. Mai yiwuwa ba za mu so mu yi wa mutum waꞌazi ba saboda yanayin jikinsa, ko inda ya fito, ko iliminsa, ko irin rayuwar da yake yi, ko kuma addininsa. Amma ka tuna cewa:
-
Jehobah da Yesu ne kawai suke sanin abin da ke zuciyar mutane, mu ba za mu iya yin hakan ba.
-
Kada mu ɗauka cewa Jehobah ba zai iya nuna ma wasu mutane jinƙai ba.
5. Ka yi ƙarfin hali, amma ka daraja mutane kuma ka kasance da wayo. (Mat. 10:16) Ka guji yin gardama. Ka kyale mutumin idan ba ya so ya saurare ka, ko idan ka ga cewa ci gaba da tattaunawar zai sa ka cikin matsala.—K. Mag. 17:14.
KA KUMA KARANTA
A. M. 4:31; Afis. 6:19, 20; 2 Tim. 1:7