DARASI NA 16
Mene Ne Aikin Bawa Mai Hidima
Littafi Mai Tsarki ya ambata rukuni biyu na mazaje Kiristoci waɗanda suke kula da ayyukan da ake gudanarwa a cikin ikilisiya, su ne, ‘masu kula da ikilisiya da kuma bayi masu hidima.’ (Filibiyawa 1:1, Littafi Mai Tsarki) Akwai dattawa da bayi masu hidima da dama da suke hidima a ikilisiyoyi dabam-dabam. Wane aiki ne bayi masu hidima suke yi a madadinmu?
Suna taimaka wa rukunin dattawa. Bayi masu hidima ’yan’uwa ne matasa da tsofaffi, waɗanda aka amince da su, suna da dangantaka mai kyau da Allah, kuma suna aiki da zuciya ɗaya. Suna kula da muhimman ayyuka dabam-dabam a cikin ikilisiya da ba su ƙunshi aikin koyarwa da kuma kai ziyara ta ƙarfafawa ba. Hakan yana ba dattawa zarafin mai da hankali ga koyarwa da kuma kai ziyara ta ƙarfafawa.
Suna yin hidima masu amfani. An ba wasu daga cikin bayi masu hidima aikin marabtar waɗanda suka zo taro kuma su ba su wurin zama. Wasu kuma suna kula ne da kayan sautin ko rarraba littattafai, wasu suna kula da kuɗin ikilisiya ko kuma ba da yanki ga waɗanda za su fita yin wa’azi. Suna kuma taimakawa wajen kula da Majami’ar Mulki. Dattawa suna iya ba su aikin taimaka wa tsofaffi. A shirye bayi masu hidima suke su yi duk wani aikin da aka ba su, kuma ’yan’uwa a cikin ikilisiya suna daraja su saboda sadaukarwar da suka yi da kuma ƙwazon da suke da shi.—1 Timotawus 3:13.
Suna kafa misali mai kyau a matsayin Kiristoci mazaje. Ana naɗa bayi masu hidima ne domin halaye masu kyau na Kirista da suke nunawa. Suna ƙarfafa bangaskiyarmu sa’ad da suke gudanar da jawabai dabam-dabam a taro. Saboda misali mai kyau da suka kafa wajen yin wa’azi, suna taimaka mana mu ƙara kasancewa da ƙwazo a hidima. Saboda haɗin kai da suke ba dattawa, suna kyautata farin ciki da haɗin kan da ke tsakaninmu. (Afisawa 4:16) Da sannu-sannu, su ma wata rana za su cancanta su zama dattawa.
-
Waɗanne irin mazaje ne bayi masu hidima?
-
Ta yaya bayi masu hidima suke taimakawa don abubuwa su guduna sumul a cikin ikilisiya?