DARASI NA 25
Me Ya Sa Ake Gina Majami’un Mulki Kuma Yaya Ake Yin Ginin?
Kamar yadda sunan nan Majami’ar Mulki ya nuna, ainihin cibiyar abin da ake koyarwa a wurin daga Littafi Mai Tsarki, shi ne, Mulkin Allah, kuma shi ne ainihin abin da Yesu ya koyar a duniya.—Luka 8:1.
Cibiyoyi ne inda ake bauta ta gaskiya a yanki. Shaidun Jehobah suna tsara aikin da suke yi na wa’azi a Majami’ar Mulki da ke yankinsu. (Matta 24:14) Girma da fasalin Majami’un Mulki sukan bambanta, amma gini ne madaidaici inda ikilisiya guda ko sama da haka suke yin taro. Saboda ƙaruwar da ake samu na ikilisiyoyi da masu shela, a cikin ’yan shekarun nan, mun gina dubban sababbin Majami’un Mulki (wajen guda biyar a kowace rana). Ta yaya ake cim ma hakan?—Matta 19:26.
An gina su ne da gudummawar da mutane suka ba da don gina Majami’un Mulki. Ana tura gudummawar nan ta kuɗi zuwa ofishin reshe don ya ba ikilisiyoyin da suke son su gina ko su gyara Majami’ar Mulki.
Masu ginin suna yin sa ne da son rai ba tare da an biya su ko sisi ba kuma mutane ne daga wurare dabam-dabam. A ƙasashe da yawa, akwai Rukunin Masu Gina Majami’ar Mulki. Wannan rukunin na magina tare da ’yan’uwan da suke taimaka musu suna zuwa ikilisiyoyi dabam-dabam a birane da ƙauyuka a ƙasar da suke hidima, don su taimaka wa ikilisiyoyi wajen gina sababbin Majami’un Mulki. A wasu ƙasashe, an zaɓi Shaidun da suka ƙware don su riƙa duba ayyukan gina da kuma gyara Majami’un Mulki da ke yankin da aka ba su. Ko da yake ƙwararrun magina daga yankin suna ba da kansu, yawancin masu aikin ’yan ikilisiyar da ake yi wa ginin ne. Ruhun Jehobah da kuma ƙoƙarin da mutanensa suke yi da zuciya ɗaya ne ya sa hakan ya yiwu.—Zabura 127:1; Kolosiyawa 3:23.
-
Me ya sa ake kiran wuraren da muke ibada Majami’ar Mulki?
-
Yaya ake gina Majami’un Mulki a faɗin duniya?