Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | WACE KYAUTA CE TA FI TAMANI?

“Wannan Ce Kyauta Mafi Daraja Da Aka Taba Ba Ni”

“Wannan Ce Kyauta Mafi Daraja Da Aka Taba Ba Ni”

Abin da wata yarinya ’yar shekara 13 ta ce ke nan lokacin da aka ba ta kyautar wani ɗan kare. Wata ’yar kasuwa kuma ta ce kwamfutar da mahaifinta ya ba ta tun lokacin da take makarantar jami’a ce kyautar da ta canja rayuwarta. Wani mutum da ya yi sabon aure kuma ya ce katin bikin cika shekara ɗaya da aure da matarsa ta yi da kanta ne kyauta mafi daraja da ya taɓa samu.

A kowace shekara, mutane suna ƙoƙarin neman kyauta “mafi daraja” da za su ba abokansu ko kuma danginsu. Kuma da yawa cikinsu za su so su ji ra’ayoyin waɗanda suka ba kyautar kamar waɗanda aka ambata da farko. Kai fa? Za ka so ka karɓi kyautar da ke da daraja ko kuma ka ba da kyauta mai daraja?

Wannan abu ne mai muhimmanci, domin hakan zai sa wanda ya karɓi kyautar da kuma wanda ya ba da kyautar farin ciki. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bayarwa ta fi karɓa albarka.” (Ayyukan Manzanni 20:35) Hakika, za mu yi farin ciki sosai idan wanda muka ba kyauta ya ɗauke ta da tamani.

Me za ka yi don kyautar da ka bayar ta sa kai da kuma wanda ka ba kyautar farin ciki? Idan kuma ba za ka iya ba da kyauta “mafi daraja” ba, me za ka iya yi domin kyautarka ta zama da daraja ga wanda ya karɓa?