Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Idan Wani Ya Ci Amanar Aure

Idan Wani Ya Ci Amanar Aure

Maria, daga ƙasar Sifen ta ce: “Na ji baƙin ciki sosai a lokacin da mijina ya ce zai sake ni don ya auri wata budurwa. Na yi baƙin ciki sosai domin ya cuce ni, musamman ma idan na tuna irin taimakon da na yi masa.”

Bill, daga ƙasar Sifen ya ce: “Sa’ad da matata ta bar ni, na ji kamar wata gaɓar jikina ta mutu. Abubuwan da muke burin yi da begenmu duk sun zama banza. A wasu lokatai, nakan ji kamar na daina baƙin ciki, amma kafin in ankara sai na soma baƙin ciki kuma.”

CIN AMANA yana jawo baƙin ciki sosai. Wasu ma’aurata sun gafarta wa juna bayan haka kuma suka ci gaba da zaman lafiya. * Amma ko sun ci gaba da zama tare ko a’a, wanda aka ci amanarsa zai yi fama da baƙin ciki. Ta yaya irin waɗannan mutanen za su iya jimrewa?

NASSOSIN DA ZA SU IYA TAIMAKAWA

Mutane da yawa da aka ci amanarsu sun sami ƙarfafa daga Littafi Mai Tsarki. Sun gane cewa Allah yana sane da baƙin cikin da suke ciki kuma yana tausaya musu.​—Malakai 2:​13-16.

“Sa’ad da damuwoyi sukan yi mini yawa, ta’aziyyarka takan ƙarfafa raina.”​Zabura 94:19.

Bill ya ce: “A lokacin da na karanta wannan ayar, na yi tunanin yadda Jehobah yake ƙarfafa ni kamar yadda uba mai ƙauna yake yi wa yaransa.”

“Kakan nuna kanka mai ƙauna.”​Zabura 18:25.

Carmen da mijinta ya ci amanarta ta ce: “Ko da yake maigidana ya ci amanata, na tabbata cewa Jehobah zai kasance tare da ni kuma ba zai taɓa kunyatar da ni ba.”

“Kada ku damu da kome, sai dai a cikin kome ku faɗa wa Allah bukatunku ta wurin addu’a. . . . Ta haka kuwa Allah zai ba ku salama iri wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam, za ta kuma tsare zukatanku.”​Filibiyawa 4:​6, 7.

Sasha ta ce: “Na karanta ayoyin nan a kai a kai kuma da na nace a addu’a, Jehobah ya taimaka min in kasance da kwanciyar hankali.”

Duka waɗanda muka ambata su a baya sun ji cewa ba za su iya jimre wa ba a wasu lokatai. Amma sun dogara ga Jehobah kuma Kalmarsa ta ƙarfafa su. Bill ya ce: “Bangaskiyar da nake da ita ta taimaka min in yi rayuwa mai ma’ana duk da damuwar da na shiga. Kuma Jehobah ya kasance tare da ni ‘ko da na bi ramin duhun mutuwa.’”​—Zabura 23:4.

^ sakin layi na 4 Don samun ƙarin bayani game da ko ya dace a gafarta ko a’a, ka duba jerin talifofin Awake! na 22 ga Afrilu, 1999, mai jigo “When a Mate Is Unfaithful,” wato Idan Wani Ya Ci Amanar Aure.