TALIFIN NAZARI NA 14
Kana Cika Hidimarka ga Allah Kuwa?
“Ka cika hidimarka na zaman bawan Allah.”—2 TIM. 4:5.
WAƘA TA 57 Ku Yi wa Dukan Mutane Wa’azi
ABIN DA ZA A TATTAUNA *
1. Mene ne dukan bayin Allah suke son yi, kuma me ya sa? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)
YESU KRISTI ya umurci mabiyansa cewa “ku je . . . ku faɗa wa dukan al’umman duniya su bi ni, ku sa su zama almajiraina.” (Mat. 28:19) Dukan bayin Allah suna so su koya yadda za su ‘cika hidimar’ nan da aka ce su yi. (2 Tim. 4:5) Ballantana ma wannan shi ne aikin da ya fi muhimmanci kuma muna bukatar mu yi shi da gaggawa. Amma yana iya yi mana wuya mu yi hidimar yadda muke so.
2. Waɗanne ƙalubale ne muke fuskanta yayin da muke ƙoƙarin cika hidimarmu?
2 Da akwai wasu ayyuka masu muhimmanci da ke ɗaukan lokacinmu da kuma gajiyar da mu. Wataƙila muna bukatar mu ɗau sa’o’i muna aiki don mu biya bukatunmu da na iyalinmu. Ko kuma wataƙila muna fama da wasu matsaloli a iyalinmu ko rashin lafiya ko baƙin ciki ko kuma tsufa. Ta yaya za mu cika hidimarmu yayin da muke fama da waɗannan matsalolin?
3. Kamar yadda Matiyu 13:23 ya nuna, waɗanne ƙalubale ne wasu suke fuskanta?
3 Idan yanayinmu yana hana mu yin ƙwazo sosai a hidimarmu ga Jehobah, kada mu yi sanyin gwiwa. Yesu ya san cewa sa’o’in da za mu yi muna wa’azi zai bambanta. (Karanta Matiyu 13:23.) Jehobah yana daraja kome da muke yi a hidimarsa. (Ibran. 6:10-12) A wani bangare kuma, yanayinmu yana iya ba mu zarafin ƙara faɗaɗa hidimarmu. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu sa hidimarmu ta zama abu mafi muhimmanci, mu sauƙaƙa salon rayuwarmu kuma mu inganta wa’azinmu da koyarwarmu. Amma da farko, mene ne cika hidimarmu take nufi?
4. Mene ne cika hidimarmu yake nufi?
4 Cika hidimarmu tana nufin cewa muna bukatar mu yi wa’azi da kuma koyarwa gwargwadon ƙarfinmu. Amma hakan ba ya nufin yawan sa’o’in da muke yi kawai a wa’azi ba. Dalilin da ya sa muke wa’azi yana da muhimmanci ga Jehobah. Muna yin ƙwazo sosai a hidimarmu domin muna ƙaunar Jehobah da kuma maƙwabtanmu. * (Mar. 12:30, 31; Kol. 3:23) Bauta wa Allah da ƙwazo yana nufin yin amfani da dukan ƙarfinmu a hidimarmu ga Allah. Idan muka fahimci cewa yin wa’azi gata ce babba, hakan zai motsa mu mu yi iya ƙoƙarinmu don mu yaɗa bishara ga mutane da yawa.
5-6. Ka ba da misalin da ya nuna yadda mutumin da bai da lokaci sosai zai iya sa yin wa’azi ya zama abu mafi muhimmanci.
5 Ka yi la’akari da misalin nan. Wani matashi yana son koyarwa sosai, kuma yana jin daɗin yin hakan a duk lokacin da ya sami zarafi. Daga baya, sai ya soma koyarwa a makaranta a kowane ƙarshen mako. Amma albashinsa ba ya biyan bukatunsa. Don haka, sai ya nemi aiki a wani kanti kuma yana yin wannan aikin daga ranar Litinin zuwa Jumma’a. Duk da cewa yana yin amfani da yawancin lokacinsa a kantin, ya fi son aikin koyarwa. Yana so ya ƙware a koyarwa sosai kuma ya riƙa aikin koyarwa a kowane lokaci. Saboda haka, yana yin amfani da kowace damar da ya samu don ya yi koyarwa ko da na ɗan lokaci ne.
6 Hakazalika, wataƙila ba ka da zarafin yin wa’azi yadda kake so. Duk da haka, abin da ka fi son yi ke nan. Kana yin ƙoƙarin inganta yadda kake wa’azi don ka ratsa zuciyar mutane. Da yake kana da ayyuka da yawa, kana iya yin tunanin yadda za
ka sa yin wa’azi ya zama abin da ya fi muhimmanci a gare ka.YADDA ZA KA SA HIDIMARKA TA FI MUHIMMANCI A GARE KA
7-8. Ta yaya za mu yi koyi da Yesu a wa’azinmu?
7 Yesu ya kafa misali mai kyau ta yadda ya ɗauki yin wa’azi. Yin shela game da Mulkin Allah ne ya fi muhimmanci a rayuwarsa. (Yoh. 4:34, 35) Ya yi tafiya mai nisa don ya yi wa mutane da dama wa’azi. Ya yi amfani da dukan zarafin da ya samu don ya tattauna da mutane a gidajensu ko kuma duk inda ya same su. Yesu ya sa yin wa’azi a kan gaba a rayuwarsa.
8 Muna iya yin koyi da Yesu ta wajen neman zarafin yi wa mutane wa’azi game da Mulkin Allah a duk inda muka same su. Muna a shirye mu yi sadaukarwa don mu yi wa’azi. (Mar. 6:31-34; 1 Bit. 2:21) Wasu a ikilisiya suna yin hidimar majagaba na musamman ko na kullum ko kuma na ɗan lokaci. Wasu sun koyi sabon yare don su yi wa’azi ko kuma sun ƙaura zuwa inda ake bukatar masu shela. Duk da haka, masu shela da ba sa yin irin waɗannan hidimar ne suke yin yawancin wa’azin da ake yi. Ko da wane irin yanayi ne muke ciki, Jehobah ba ya bukatar mu yi abin da ya fi ƙarfinmu. Yana so dukanmu mu ji daɗin wa’azin “labari mai daɗi, mai daraja na Allah mai albarka” da muke yi.—1 Tim. 1:11; M. Sha. 30:11.
9. (a) Ta yaya Bulus ya fi mai da hankali ga yin wa’azi, har a lokacin da yake aikin tanti? (b) Ta yaya Ayyukan Manzanni 28:16, 30, 31 ya nuna cewa Bulus ya ɗauki yin wa’azi da muhimmanci?
9 Manzo Bulus ya kafa misali mai kyau ta wurin sa yin wa’azi ya zama abin da ya fi muhimmanci a gare shi. Bulus bai da kuɗi sosai a lokacin da ya je yin wa’azi a Korinti a ƙaro na biyu. Don haka, ya soma yin tanti, amma yin tanti ba shi ne abin da fi muhimmanci a gare shi ba. Yana yin wannan aikin ne don ya sami abin biyan bukatunsa yayin da yake wa Korintiyawa wa’azi “kyauta.” (2 Kor. 11:7) Ko da Bulus ya yi aiki don ya biya bukatunsa, ya ci gaba da ɗaukan yin wa’azi da muhimmanci kuma ya yi wa’azi a kowace ranar Assabaci. Da zarar Bulus ya sami isashen kuɗi, ya “ba da dukan lokacinsa a kan yin wa’azi, yana tabbatar wa Yahudawa cewa Yesu shi ne Almasihu.” (A. M. 18:3-5; 2 Kor. 11:9) Daga baya sa’ad da aka tsare Bulus har tsawon shekara biyu a Roma, ya yi wa’azi ga waɗanda suka kawo masa ziyara kuma ya rubuta wasiƙu. (Karanta Ayyukan Manzanni 28:16, 30, 31.) Bulus bai bar kome ya hana shi mai da hankali ga yin wa’azi ba. Ya rubuta cewa: “Da yake muna da wannan hidima . . . , ba za mu fid da zuciya ba.” (2 Kor. 4:1) Kamar Bulus, ko da muna aiki na sa’o’i da yawa don mu biya bukatunmu, muna iya sa yin wa’azi ya zama abin da ya fi muhimmanci a gare mu.
10-11. Ta yaya za ka iya cim ma hidimarka idan kana rashin lafiya?
10 Idan ba ma iya yin wa’azi gida-gida yadda muke so, wataƙila don mun tsufa ko kuma muna rashin lafiya, muna iya yin wa’azi a wasu hanyoyi. Kiristoci a ƙarni na farko sun yi amfani da dukan zarafin da suka samu don su yi wa’azi. Sukan yi hakan gida-gida ko inda jama’a suke ko sa’ad da suke yin ayyukansu na yau da kullum ga ‘waɗanda suke samu.’ (A. M. 17:17; 20:20) Idan ba ma iya yin wa’azi a wurare masu nisa, muna iya zama a wurin da jama’a suke don mu yi wa mutanen da ke wucewa wa’azi. Ƙari ga haka, muna iya yin wa’azi sa’ad da muke yin ayyukanmu na yau da kullum ko mu rubuta wasiƙa ko kuma mu yi wa’azi ta waya. Masu shela da yawa da ba sa iya yin wa’azi gida-gida don suna rashin lafiya ko kuma suna fuskantar wata matsala dabam, suna jin daɗin yin wa’azi a waɗannan hanyoyin.
11 Duk da cewa kana fama da rashin lafiya, kana iya cika hidimarka. Ka sake yin la’akari da misalin manzo Bulus. Ya ce: “Zan iya yin kome ta wurin . . . wanda yake ƙarfafa ni.” (Filib. 4:13) Bulus ya bukaci wannan ƙarfafawar sa’ad da ya yi rashin lafiya a wani lokacin da ya je wa’azi a ƙasar waje. Ya gaya wa Galatiyawa cewa: “Rashin lafiyar da na yi, ya buɗe hanyar da na kawo muku labari mai daɗi da farko.” (Gal. 4:13) Hakazalika, rashin lafiyarka tana iya ba ka zarafin yin wa’azi ga likitoci da nas da kuma masu kula da kai. Ba a samun yawancin mutanen nan a gida sa’ad da masu shela suka je wa’azi.
YADDA ZA KA SAUƘAƘA SALON RAYUWARKA
12. Mene ne furucin nan “idan idonka yana da lafiya” yake nufi?
12 Yesu ya ce: “Ido shi ne fitilar jiki, idan idonka yana da lafiya, dukan jikinka ma zai cika da haske.” (Mat. 6:22) Mene ne Yesu yake nufi? Yana nufin cewa kada mu yarda wani abu ya raba hankalinmu amma mu sauƙaƙa salon rayuwarmu ko kuma mu mai da hankali ga maƙasudin da muka kafa. Yesu ya kafa misali mai kyau domin ya mai da hankali sosai a hidimarsa, kuma ya koya wa mabiyansa su mai da hankali ga bauta wa Jehobah da kuma goyon bayan Mulkinsa. Muna bin misalin Yesu ta wurin sa hidimarmu ta zama abu mafi muhimmanci, wato ‘miƙa kanmu ga al’amuran mulkinsa, da kuma aikata adalcinsa.’—Mat. 6:33.
13. Mene ne zai taimaka mana mu mai da hankali a hidimarmu?
13 Hanya ɗaya da za mu iya mai da hankali ga hidimarmu ita ce ta sauƙaƙa salon rayuwarmu. Yin hakan zai ba mu damar taimaka wa mutane su san Jehobah kuma su ƙaunace shi. * Alal misali, za ka iya rage ayyukan da kake yi don ka sami damar ƙara ƙwazo a wa’azi. Ko kuma ka rage yin shaƙatawar da ke cin lokaci sosai.
14. Waɗanne canje-canje ne wasu ma’aurata suka yi don su mai da hankali ga hidimarsu?
14 Abin da wani dattijo mai suna Elias da matarsa suka yi ke nan. Ya ce: “Ba mu soma yin hidimar majagaba nan da nan ba, amma mun ɗauki wasu matakai don mu sami zarafin ƙara ƙwazo a wa’azi. Alal misali, mun rage kashe kuɗi, kuma mun rage yawan shaƙatawar da muke yi. Ƙari ga haka, mun gaya wa shugaban aikinmu cewa ya yi gyara ga tsarin ayyukanmu don mu sami lokacin yin wa’azi. A sakamako, mun soma fita wa’azi da yamma, kuma muka soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa. Bugu da ƙari, mun soma fita wa’azi a tsakiyar mako sau biyu a kowane wata. Hakan ya sa mu farin ciki sosai!”
YADDA ZA KA INGANTA WA’AZINKA DA KUMA KOYARWARKA
15-16. Kamar yadda littafin 1 Timoti 4:13, 15 ya nuna, ta yaya za mu ci gaba da inganta wa’azinmu? (Ka duba akwatin nan “ Maƙasudan da Za Su Taimaka Min In Cim ma Hidimata.”)
15 Wata hanya kuma da za mu iya cim ma hidimarmu ita ce ta wajen inganta K. Mag. 1:5; karanta 1 Timoti 4:13, 15.
yadda muke wa’azi da kuma koyarwa. A wasu wurare, ana koyar da ma’aikata a kai a kai don su ƙara samun ilimi kuma su inganta aikinsu. Haka ma yake da masu shelar Mulkin Allah. Muna bukatar mu ci gaba da koyon yadda za mu ƙware a hidimarmu.—16 Amma ta yaya za mu ci gaba da koyan yadda za mu inganta hidimarmu? Ta wajen mai da hankali ga abubuwan da ake koya mana kowane mako a Taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu. Wannan taron yana koya mana yadda za mu inganta wa’azinmu. Alal misali, muna iya koyan darasi daga shawarar da mai kujerar taron ya ba waɗanda suka yi aiki a taron. Muna iya koyan abubuwan da za mu iya yin amfani da shi a wa’azi. Muna iya yin amfani da shawarwarin sa’ad da muke wa’azi. Muna iya tambayar ɗan’uwan da ke kula da rukunin wa’azinmu ya taimaka mana ko kuma mu yi wa’azi tare da shi ko wani mai shela da ya ƙware. Ƙari ga haka, muna iya yin wa’azi tare da majagaba ko kuma mai kula da da’ira. Yayin da muka ƙware a yin amfani da Kayan Aiki don Koyarwa, za mu ji daɗin yin wa’azi da kuma koyarwa.
17. Mene ne za ka more idan ka cim ma hidimarka?
17 Muna farin ciki cewa Jehobah ya ba mu gatan zama ‘abokan aikinsa.’ (1 Kor. 3:9) Idan ka zaɓi “abin da ya fi kyau” kuma ka mai da hankali ga hidimarka, hakan zai taimaka maka ka yi wa Jehobah “hidima da murna.” (Filib. 1:10; Zab. 100:2) Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ba ka ƙarfin da kake bukata don ka cim ma hidimarka, ko da kana fama da matsaloli. (2 Kor. 4:1, 7; 6:4) Ko da kana da zarafin yin wa’azi sosai ko a’a, kana iya yin “taƙama da abin da” ka yi da dukan zuciyarka a hidimar Jehobah. (Gal. 6:4) Idan ka cim ma hidimarka, kana nuna cewa kana ƙaunar Jehobah da kuma maƙwabtanka. “In ka yi haka, za ka ceci kanka da kuma masu jinka.”—1 Tim. 4:16.
WAƘA TA 58 Muna Neman Mutane Masu Sauƙin Kai
^ sakin layi na 5 Yesu ya ba mu umurnin yin wa’azin game da Mulkin Allah da kuma almajirantarwa. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu cika hidimarmu ga Allah ko da muna fuskantar matsaloli. Ƙari ga haka, za mu tattauna yadda za mu inganta wa’azinmu kuma mu riƙa jin daɗin sa.
^ sakin layi na 4 MA’ANAR WASU KALMOMI: Hidimarmu ga Jehobah ta ƙunshi yin wa’azi da koyarwa da yin aikin gine-gine da kula da wuraren ibada da kuma aikin ba da agaji.—2 Kor. 5:18, 19; 8:4.
^ sakin layi na 13 Ka duba hanyoyi bakwai da aka ambata a akwatin nan “Yadda Za Ka Sauƙaƙa Rayuwarka” a Hasumiyar Tsaro ta Yuli 2016, shafi na 10.
^ sakin layi na 62 BAYANI A KAN HOTUNA Shafi na 6: Wata ’yar’uwa tana nuna yadda ake koma ziyara a taron tsakiyar mako. Bayan haka, tana rubuta shawarar da mai kujerar taron ya ba ta a ƙasidar nan Ka Mai da Hankali ga Karatu da Kuma Koyarwa. Ta yi amfani da darussan da ta koya sa’ad da ta fita wa’azi a ƙarshen mako.