TALIFIN NAZARI NA 43
Hikima Tana Kira da Babban Murya
“Ku ji! Hikima tana kira a kan tituna, tana tā da murya a fili na cikin gari.”—K. MAG. 1:20.
WAƘA TA 88 Ka Koya Mini Hanyoyinka
ABIN DA ZA A TATTAUNA a
1. Mene ne raꞌayin mutane da yawa game da shawarwarin da ke Littafi Mai Tsarki? (Karin Magana 1:20, 21)
A ƘASASHE da yawa, muna yawan ganin yanꞌuwanmu suna rarraba littattafanmu ga mutanen da suke wucewa a kan tituna. Ka taɓa yin irin wannan waꞌazin kuwa? Idan haka ne, ba shakka ka taɓa tunani a kan kwatancin nan da ke littafin Karin Magana da ya nuna cewa hikima tana kira a kan tituna don mutane su saurari shawararta. (Karanta Karin Magana 1:20, 21.) Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu suna ƙunshe da “hikima,” wato hikimar da take fitowa daga wurin Jehobah. Wannan ne bayanan da mutane suke bukata don su ɗauki mataki na farko wanda zai sa su sami rai na har abada. Muna farin ciki idan wani ya karɓi ɗaya daga cikin littattafanmu. Amma ba kowa ne yake karɓa ba. Wasu ba su damu su san abin da ke Littafi Mai Tsarki ba. Wasu suna yi mana dariya. A ganinsu, Littafi Mai Tsarki tsohon yayi ne. Wasu kuma suna ganin abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da dabiꞌa, ya yi tsanani, kuma suna ganin cewa waɗanda suke bin irin waɗannan dabiꞌun, ꞌyan tsattsauran raꞌayi ne. Duk da haka, Jehobah ya ci gaba da tanadar wa kowa hikimarsa. A waɗanne hanyoyi?
2. A ina ne za mu iya samun hikima a yau, amma mene ne yawancin mutane suka zaɓi su yi?
2 Hanya ɗaya da Jehobah yake tanadar mana da hikimarsa ita ce, ta wajen Littafi Mai Tsarki. Kusan kowa yana da damar samun littafin nan. Littattafanmu da ke bayyana abin da ke Littafi Mai Tsarki kuma fa? Mun gode wa Jehobah, domin da taimakonsa muna da littattafan nan a yaruka fiye da dubu. Waɗanda suka karanta kuma suka bi abin da ke ciki, za su amfana. Amma mutane da yawa sun zaɓi su yi watsi da wannan hikima daga Jehobah. Idan suna so su yanke wata shawara, sukan bi raꞌayinsu ko kuma su bi raꞌayin wasu mutane. Za su iya yi mana baꞌa don mun zaɓi mu bi shawarar da ke Littafi Mai Tsarki. Za a tattauna dalilin da ya sa mutane suke yin haka a wannan talifin. Bari mu fara da tattauna yadda za mu iya samun hikima daga Jehobah.
SANIN JEHOBAH YANA SA MU ZAMA MASU HIKIMA
3. Me ya kamata mu yi don mu zama masu hikima?
3 Idan muna amfani da abin da muka sani don mu yanke shawara mai kyau, hakan zai nuna cewa muna da hikima. Amma hikima ta gaskiya ta wuce hakan. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Tsoron Yahweh shi ne mafarin hikima, sanin Mai Tsarkin nan kuwa ganewa ne.” (K. Mag. 9:10) Saboda haka, idan muna so mu yanke wata shawara mai muhimmanci, ya kamata mu nemi raꞌayin Jehobah game da batun. Za mu iya yin hakan ta wajen bincika Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu. Hakan zai nuna cewa muna da hikima ta gaske.—K. Mag. 2:5-7.
4. Me ya sa Jehobah ne kaɗai zai iya ba mu hikima ta gaskiya?
4 Jehobah ne kaɗai zai iya sa mu zama masu hikima. (Rom. 16:27) Me ya sa muka ce shi ne tushen hikima? Na farko, a matsayinsa na Mahalicci, ya san kome game da halittunsa. (Zab. 104:24) Na biyu, dukan abubuwan da Jehobah yake yi suna nuna cewa shi mai hikima ne. (Rom. 11:33) Na uku, shawara daga wurin Jehobah takan amfani waɗanda suka bi ta. (K. Mag. 2:10-12) Idan muna so mu kasance masu hikima, wajibi ne mu amince da abubuwan nan guda uku da muka faɗa kuma mu yi amfani da su saꞌad da muke yanke shawarwari.
5. Wane sakamako ne mutane za su samu idan sun ƙi su amince cewa Jehobah shi ne Tushen hikima?
5 Da yawa cikin waɗanda muke haɗuwa da su a waꞌazi, sun amince cewa abubuwan da suke gani a duniya suna da kyau sosai. Amma ba su yarda cewa akwai Mahalicci ba. Wasu kuma da muke haɗuwa da su, sukan ce sun yarda cewa akwai Allah, amma suna ganin abubuwan da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa tsohon yayi ne, kuma sukan zaɓi su bi raꞌayinsu kawai. Mene ne sakamakon hakan? Shin, duniya ta gyaru don mutane suna bin raꞌayinsu maimakon na Allah? Hakan ya sa su farin ciki ko ya ba su bege? Abubuwan da muke gani kewaye da mu sun tabbatar mana cewa: “Babu hikima, ko ganewa, ko shawara wadda za ta ci nasara a kan Yahweh.” (K. Mag. 21:30) Hakan yana ƙarfafamu mu ci gaba da roƙon Jehobah ya ba mu hikima! Abin baƙin cikin shi ne, yawancin mutane ba sa hakan. Me ya sa?
DALILIN DA YA SA MUTANE SUKE WATSI DA HIKIMA TA GASKIYA
6. Bisa ga Karin Magana 1:22-25, su waye ne suke yin watsi da hikima ta gaskiya?
6 Mutane da yawa ba sa amsawa saꞌad da hikima take “kira a kan tituna.” A cikin Littafi Mai Tsarki, an ambata rukunin mutane uku da suke yin watsi da hikima kuma su ne: “Marasa tunani” da “masu reni” da kuma “wawaye.” (Karanta Karin Magana 1:22-25.) Bari mu ga halayen da suke sa irin mutanen nan su yi watsi da hikima ta gaskiya da kuma yadda za mu guji zama kamar su.
7. Me ya sa wasu mutane suka zaɓi su zama “marasa tunani”?
7 Marasa tunani, su ne suke amince da duk abin da aka gaya musu kuma ana saurin ruɗinsu. (K. Mag. 14:15) Muna yawan haɗuwa da irin mutanen nan a waꞌazi. Alal misali, ka yi laꞌakari da miliyoyin mutanen da shugabannin addinai da na siyasa suke ruɗinsu. Wasu sukan yi mamaki sosai bayan sun gane cewa ruɗinsu ne shugabannin nan suka yi. Amma waɗanda aka ambata a Karin Magana 1:22, sun zaɓi su zama marasa tunani da kansu don suna jin daɗin hakan. (Irm. 5:31) Suna yin abin da suka ga dama kuma ba sa so su koyi abin da ke Littafi Mai Tsarki ko kuma su yi biyayya da dokokin da ke ciki. Mutane da yawa suna kamar wata mata mai son addini da ke Quebec, Kanada, wadda ta gaya ma wani Mashaidi cewa: “Idan malamin addininmu ya ruɗe mu, laifinsa ne ba namu ba!” Ba shakka, ba za mu yi koyi da irin mutanen nan da suka zaɓi su zama marasa tunani da son ransu ba.—K. Mag. 1:32; 27:12.
8. Me zai taimaka mana mu zama masu tunani?
8 Akwai dalili mai kyau da ya sa Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu cewa kada mu zama marasa tunani, amma mu “zama da tunani irin na manya.” (1 Kor. 14:20) Za mu iya zama masu tunani ta wajen bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki a rayuwarmu. Idan mun yi hakan, za mu ga yadda Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu guji matsaloli kuma mu riƙa yanke shawarwari masu kyau. Zai dace mu riƙa tunani a kan shawarwarin da muke yankewa. Alal misali, idan muna nazarin Littafi Mai Tsarki kuma muna halartan taro, amma har ila ba mu yi alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma ba, zai dace mu yi tunani mu ga abin da zai taimaka mana mu cim ma wannan maƙasudin. Idan kuma mun riga mun yi baftisma, muna yin iya ƙoƙarinmu mu inganta yadda muke waꞌazi da kuma koyarwa? Shawarwarin da muke yankewa suna nuna cewa muna bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki? Muna nuna halaye masu kyau a shaꞌaninmu da mutane? Idan akwai inda muke bukatar gyara, zai dace mu yi tunani sosai a kan ƙaꞌidodin Jehobah da suke sa marar tunani ya sami hikima.—Zab. 19:7.
9. Ta yaya “masu reni” ko masu baꞌa suka nuna cewa sun yi watsi da hikima?
9 Rukuni na biyu da suke watsi da hikima ta gaskiya su ne, “masu reni.” A wasu lokuta, muna haɗuwa da irin mutanen nan a waꞌazi. Suna jin daɗin yi ma wasu baꞌa. (Zab. 123:4) Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi cewa a kwanaki na ƙarshe, za a sami masu baꞌa da yawa. (2 Bit. 3:3, 4) Kamar surukan Lutu, wasu mutane da yawa ba sa damuwa da gargaɗin da muke samu daga wurin Allah. (Far. 19:14) Mutane da yawa suna yi wa waɗanda suke bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki dariya. Masu baꞌan suna yin haka ne domin suna so “su bi irin tasu shaꞌawa wadda ba ta hali iri na Allah ba.” (Yahu. 7, 17, 18) Yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta masu baꞌan, ya yi daidai da halayen ꞌyan ridda da kuma waɗanda suka yi watsi da Jehobah.
10. Bisa ga Zabura 1:1, ta yaya za mu guji halin masu yin baꞌa?
10 Ta yaya za mu guji bin raꞌayin masu baꞌa? Hanya ɗaya ita ce, mu guji yin abota da masu yawan gunaguni. (Karanta Zabura 1:1.) Hakan yana nufin cewa bai kamata mu riƙa sauraron ko karanta wani abu daga wurin ꞌyan ridda ba. Ya kamata mu mai da hankali don mu guji yawan gunaguni da shakkar abubuwan da Jehobah yake yi da kuma umurnan da yake ba mu ta ƙungiyarsa. Don mu guji yin hakan, zai dace mu tambayi kanmu: ‘Ina yawan yin gunaguni idan aka ba mu wani sabon umurni ko bayani? Ina yawan gani cewa waɗanda suke mana ja-goranci suna da matsala?’ Idan mun yi saurin daina halayen nan, Jehobah zai yi farin ciki da mu.—K. Mag. 3:34, 35.
11. Yaya “wawaye” suke ganin ƙaꞌidodin Jehobah game da dabiꞌa?
11 Rukuni na uku da suke yin watsi da hikima su ne “wawaye.” Su wawaye ne domin sun ƙi su bi ƙaꞌidodin Allah. Suna yin abin da suka ga dama. (K. Mag. 12:15) Irin waɗannan mutanen suna watsi da Jehobah wanda shi ne tushen hikima. (Zab. 53:1) Idan mun haɗu da irin mutanen nan a waꞌazi, suna ganin kamar yadda muke bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki ba daidai ba ne. Amma ba za su iya ba mu shawarar da za ta taimaka mana a rayuwa ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Hikima tana da zurfin ganewa ga wawa, a wurin taruwa a ƙofar gari, ba shi da abin da zai faɗa.” (K. Mag. 24:7) Babu shawara mai kyau da wawaye za su iya ba mu. Shi ya sa Jehobah ya gargaɗe mu cewa mu “yi nisa daga wurin wawa.”—K. Mag. 14:7.
12. Me zai taimaka mana mu guji bin halin wawaye?
12 Mu ba kamar waɗanda suka tsani bin shawara daga Allah ba ne. Maimakon haka, muna koyan yadda za mu riƙa bin raꞌayin Allah da kuma ƙaꞌidodinsa game da dabiꞌa. Abin da zai taimaka mana shi ne mu riƙa laꞌakari da sakamakon da ake samu idan mutane suka yi masa biyayya ko suka ƙi yin hakan. Ku yi laꞌakari da matsalolin da mutane suke faɗawa a ciki don sun ƙi bin shawarwarin da muke samu daga wurin Jehobah. Saꞌan nan ku lura da yadda rayuwarku ta kasance da kyau domin kuna yi wa Allah biyayya.—Zab. 32:8, 10.
13. Jehobah yana tilasta mana mu bi shawarar da yake bayarwa ne?
13 Jehobah ya ba wa kowa dama ya zama mai hikima, amma ba ya tilasta wa kowa ya amince da hakan. Sai dai ya faɗi sakamakon da mutum zai samu idan ya ƙi ya yi amfani da hikima. (K. Mag. 1:29-32) Waɗanda suka ƙi su yi wa Jehobah biyayya ‘za su girbi sakamakonsu.’ Daga baya, za su fuskanci matsaloli da dama kuma a ƙarshe Jehobah zai hallaka su. Akasin haka, Jehobah ya yi alkawari ma waɗanda suke saurarar shawarar da yake bayarwa kuma suke aikatawa cewa: “Waɗanda suka saurare ni za su zauna lafiya. Za su kuwa zauna rai a kwance, babu tsoron azaba.”—K. Mag. 1:33.
HIKIMA TA GASKIYA TANA AMFANE MU
14-15. Me muka koya daga Karin Magana 4:23?
14 Idan muka bi hikimar Allah, babu shakka za mu amfana. Kamar yadda muka tattauna, Jehobah ya tanadar da hikimarsa a sauƙaƙe. Alal misali, a cikin littafin Karin Magana, Jehobah ya ba mu shawarwari masu kyau da za su taimaka mana a rayuwa idan mun bi su. Bari mu tattauna misalai huɗu na irin shawarwarin nan.
15 Ka kiyaye tunanin zuciyarka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kiyaye zuciyarka da dukan iyakacin ƙoƙari, gama daga cikinta rai yake fitowa kamar ruwa.” (K. Mag. 4:23) Ka yi laꞌakari da yadda mutum yake kula da zuciyarsa. Don mu kula da ita, muna bukatar mu ci abincin da zai gina mana jiki, mu riƙa motsa jiki kuma mu guji halaye marasa kyau. Haka ma muke kāre tunanin zuciyarmu. Muna karanta Kalmar Allah kullum. Mukan yi shiri kafin mu halarci taro kuma mu halarci taron. Ƙari ga haka, mukan ba da kalamai a taron. Muna yin waꞌazi babu fashi. Kuma muna guje wa halaye marasa kyau ta wajen ƙin yin abubuwan da za su iya ɓata tunanin zuciyarmu kamar nishaɗi marasa kyau da kuma abokan banza.
16. Ta yaya Karin Magana 23:4, 5 suke taimaka mana a yau?
16 Ka gamsu da abin da kake da shi. Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu cewa: “Kada ka gajiyar da kanka garin neman dukiya, . . . saꞌad da ka kafa ido a kanta, za ta shuɗe. Ba shakka takan yi fikafikai ta tashi a sama kamar gaggafa.” (K. Mag. 23:4, 5) Bai da wuya mutum ya rasa dukiyarsa ko kuma abin da ya mallaka. Duk da haka, masu kuɗi da talakawa a yau sun duƙufa wajen neman kuɗi ido a rufe. Hakan yana yawan shafan yadda suke yin abubuwa har ma ya ɓata sunansu da dangantakarsu da wasu da kuma lafiyar jikinsu. (K. Mag. 28:20; 1 Tim. 6:9, 10) Amma hikima tana taimaka mana mu kasance da raꞌayin da ya dace game da kuɗi. Irin raꞌayin nan yana kiyaye mu daga halin haɗama amma yakan taimaka mana mu gamsu da abin da muke da shi kuma mu yi farin ciki.—M. Wa. 7:12.
17. Ta yaya za mu sami “harshe mai hikima,” kamar yadda aka ambata a Karin Magana 12:18?
17 Ka yi tunani kafin ka yi magana. Idan ba mu mai da hankali ba, kalmominmu za su iya sa mutane baƙin ciki. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Maganar da an yi da rashin tunani tana sa rauni kamar sokin takobi, amma harshe mai hikima yakan kawo warkewa.” (K. Mag. 12:18) Za mu sa mutane su zauna lafiya da juna idan mun guji yin gulma. (K. Mag. 20:19) Idan muna so kalamanmu su riƙa ƙarfafa mutane maimakon su sa su baƙin ciki, ya kamata mu riƙa karanta da kuma tunani a kan abin da ke Littafi Mai Tsarki. (Luk. 6:45) Idan muna yawan tunani a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa, kalamanmu za su yi kama da “Maɓuɓɓugar hikima” da ke ƙarfafa mutane.—K. Mag. 18:4.
18. Ta yaya bin abin da ke Karin Magana 24:6 zai taimaka mana mu yi nasara a waꞌazi?
18 Ka riƙa bin umurni. Idan muna so mu yi nasara, wajibi ne mu bi shawarar da Littafi Mai Tsarki ya bayar cewa: “Gama ta wurin jin hikimar waɗansu ne za ka yi yaƙinka, samun shawarar mutane masu yawa zai sa a sami nasara.” (K. Mag. 24:6) Ta yaya bin ayar nan za ta sa mu ƙware a wajen waꞌazi da koyarwa? Maimakon mu riƙa waꞌazi da koyarwa yadda muka ga dama, muna yin iya ƙoƙarinmu mu bi shawarwarin da ake ba mu. Muna samun shawarwari masu kyau a taronmu inda muke koya daga wurin wasu da suke koyar da Littafi Mai Tsarki da kyau. Ƙari ga haka, ƙungiyar Jehobah tana tanadar mana da abubuwan da muke bukata, kamar littattafanmu da bidiyoyi da za su taimaka wa mutane su fahimci abin da ke Littafi Mai Tsarki. Ka koyi yadda za ka yi amfani da abubuwan nan a waꞌazi?
19. Yaya muke ɗaukan hikima daga Jehobah? (Karin Magana 3:13-18)
19 Karanta Karin Magana 3:13-18. Muna matuƙar godiya don shawarwari masu kyau da ke Kalmar Allah, domin muna amfana sosai daga shawarwarin! A wannan talifin, mun tattauna misalai na shawarwari masu kyau da za mu iya samu a littafin Karin Magana. Hakika, dukan littattafan da ke Littafi Mai Tsarki na ɗauke da shawarwari masu kyau daga wurin Jehobah. Ya kamata mu yi amfani da shawarwarinsa a duk fannonin rayuwarmu. Ba mu damu da yadda mutanen duniya suke ɗaukan hikima daga Allah ba domin muna da tabbaci cewa, “masu albarka ne waɗanda suka riƙe” hikima da hannu bibbiyu.
WAƘA TA 36 Mu Riƙa Kāre Zuciyarmu
a Hikimar da Jehobah yake bayarwa ta fi duk wata hikimar da duniyar nan take bayarwa. Za mu ga wani kwatancin da ke littafin Karin Magana, wato hikima tana ta kira da babban murya a cikin gari. Za mu tattauna yadda za mu iya samun hikima, da yadda wasu ba su damu da hikima ba, da kuma yadda za mu amfana idan mun amsa kirar.