Yadda Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka wa Maza da Suke Yawan Damuwa
Idan ana magana a kan mutum mai yawan damuwa, a kila ka yi tunanin mutumin da ke jin tsoro ainun har ba ya iya yin kome, wanda da kyar yake tashi daga kan gado da safe, ko mai yawan magana a kan matsalolin rayuwa.
Abin da wasu suke yi ke nan idan suna damuwa ainun. Amma masu bincike sun lura cewa ba kowa ne yake hakan ba, musamman maza. Rahoton wani binciken da aka yi ya nuna cewa maza “suna yawan shan giya da kwayoyi idan suka damu sosai, don haka idan muka ga cewa namiji yana yawan shan giya, mai yiwuwa damuwa ce ta shawo kansa. Kari ga haka, damuwa takan sa namiji ya yi saurin fushi.”
Hakika, ba kowane namiji ne damuwa take sa ya yi hakan ba. Amma ko da a wace hanya ce yawan damuwa take shafan mutum, ana samun karin mutane da suke fama da matsalar yawan damuwa a wannan ‘kwanakin karshe da ake shan wahala sosai.’ (2 Timoti 3:1) Idan kana fama da yawan damuwa, Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka?
Shawarwari Masu Kyau Daga Littafi Mai Tsarki don Magance Yawan Damuwa
Littafi Mai Tsarki ya ba da shawarwari da yawa da za su iya taimaka mana sa’ad da muke cikin damuwa. Ga uku daga cikinsu.
1. “Kada ku damu domin gobe, gama gobe yana zuwa da wahalolinsa, wahalolin yau sun ishe ku domin yau.”—Matiyu 6:34.
Abin da hakan yake nufi: Zai fi dacewa mutum ya guji yawan damuwa a kan abin da mai yiwuwa ya faru, mai yiwuwa kuma ba zai faru ba. A yawancin lokuta, abubuwa da muke tsoron cewa za su faru, ba sa faruwa. Wani lokaci ma sai mu ga abubuwa sun canja sun dada kyau.
Ga abin da za ka yi: Ka tuna lokacin da ka taba tsammanin cewa wani mummunar abu zai faru, amma a karshe abin bai faru hakan ba. Sai ka sake duba abubuwan da kake damuwa a kai ka ga ko da gaske za su faru hakan.
2. “Kamar yadda karfe da karfe sukan wāsa juna, haka mutum da mutum sukan gyara rayuwar juna.”—Karin Magana 27:17.
Abin da hakan yake nufi: Abokai da iyalanmu za su iya taimaka mana mu daina yawan damuwa idan muka gaya musu matsalarmu. Kila su ba mu shawara bisa ga abin da ya taba faruwa da su, ko su taimaka mana mu canja ra’ayinmu.
Ga abin da za ka yi: Ka yi tunanin wani da zai iya ba ka shawara mai kyau, kamar wani abokinka da ya taba fuskantar irin matsalar da kake ciki. Ka ce ya gaya maka abin da ya taimaka masa ko abin da ya dada bata lamarin.
3. “Ku danka masa dukan damuwarku, gama shi ne mai lura da ku.”—1 Bitrus 5:7.
Abin da hakan yake nufi: Allah ya damu da wadanda suke shan wahala. Ya ce mu gaya masa duk wani abin da ke damunmu ta yin addu’a.
Ga abin da za ka yi: Ka rubuta abubuwan da suke sa ka damuwa a kan takarda. Sai ka yi addu’a ka gaya wa Allah kowannen su, kuma ka roke shi ya taimaka maka.
Lokacin da Ba Za A Sake Damuwa Ba
Ban da shawarar da Littafi Mai Tsarki ya bayar a kan yadda za mu rage damuwa, ya yi mana alkawari cewa nan ba da dadewa ba, abubuwan da suke sa mu damuwa ba za su kasance ba. Ta yaya hakan zai faru?
Mulkin Allah zai kawar da dukan abubuwa da suke sa mu damuwa. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4) Idan Mulkin Allah ya soma sarauta a kan duniya, ko tunanin abubuwan da suka taba sa mu damuwa ba zai zo zuciyarmu ba.—Ishaya 65:17.
Irin rayuwar da “Allah mai ba da salama” yake so ka more ke nan a nan gaba. (Romawa 16:20) Ya karfafa mu da cewa: “Na san irin shirin da nake da shi domin ku. Shiri ne na alheri, ba na masifa ba, domin in ba ku sa zuciya da rayuwa ta nan gaba.”—Irmiya 29:11.
a “Yawan damuwa” da ake magana a kai a wannan talifin, yana nufin damuwa a kan rayuwar yau da kullum ne, ba irin damuwar da ta zama rashin lafiya ba. Wadanda yawan damuwa ya zama musu rashin lafiya za su bukaci su ga likita.—Luka 5:31.