Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Surasak Suwanmake/Moment via Getty Images

KU ZAUNA A SHIRYE!

Tsananin Zafi a Fadin Duniya a 2023​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Tsananin Zafi a Fadin Duniya a 2023​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

 Mutane a fadin duniya suna fama da tsananin zafi da kuma wasu matsalolin da suke faruwa don zafin. Ga wasu rahotanni:

  •   A ranar 13 ga Yuli, 2023, National Oceanic da Atmospheric Administration, U.S. Department of Commerce sun ce: “An fuskanci yanayi mai zafi sosai a watan Yuni, kuma shi ne mafi tsanani a cikin shekaru 174 da aka taba samu a duniya gabaki daya.”

  •   A ranar 13 ga Yuli, 2023, European Space Agency, ta ce: “Kasar Italiya da Spain da Faransa da Jamus da kuma Poland suna fama da tsananin zafi. Kuma ana tsammani zai iya kai maki 48 [48°C] a tsibirin Sicily da Sardinia, wannan ne yanayi mafi zafi da aka taba yi a Turai.”

  •   A ranar 17 ga Yuli, 2023, Stefan Uhlenbrook, darectan hydrology da water da kuma cryosphere a Kungiyar Meteorological na Duniya, ya ce: “Yayin da duniyar nan take dada zafi, hakan zai iya sa a sami karin ruwan sama da kuma ambaliya masu tsanani, irin da ba a taba samu ba a dā.”

 Yadda ake ba da rahotanni game da tsananin zafi ko sanyi yana damun ka kuwa? Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da wannan batun.

An annabta cewa za a yi yanayoyi masu tsanani a Littafi Mai Tsarki?

 E. Yadda ake tsananin zafi a duniya da kuma wasu matsalolin yanayi ya jitu da abin da aka annabta a Littafi Mai Tsarki za su faru a zamaninmu. Alal misali, Yesu ya annabta cewa za mu ga “abubuwa masu ban tsoro.” (Luka 21:11) Yanayoyi masu tsanani da ake yi a duniya suna sa mutane da yawa su ji tsoro cewa, lokaci na zuwa da ba abin da zai rage a duniya.

Akwai lokacin da ba abin da zai rage a duniya?

 Aꞌa. Allah ya halicci duniyar nan ne don ta zama gidanmu na din-din-din; ba zai bar mutane su halaka ta ba. (Zabura 115:16; Mai-Wa’azi 1:4) Allah ya yi alkawari cewa zai “halaka masu halaka duniya!”​—Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 11:18.

 Littafi Mai tsarki ya nuna cewa Allah zai iya kāre duniya daga yanayoyi masu tsanani kuma zai yi hakan.

  •   “[Allah] ya kwantar da iska mai karfi, rakuman ruwa kuma suka kwanta shiru.” (Zabura 107:29) Allah yana da ikon kāre duniyar nan daga duk wani abin da zai iya jawo balaꞌi. Zai iya magance matsalolin mahalli da ke sa mutane shan wahala.

  •   “Kana kula da kasa ta wurin ba da ruwan sama, ka sa ta ba da amfani mai yawa.” (Psalm 65:9) Allah zai yi wa kasa albarka har ta dawo aljanna.

 Idan kana so ka koyi game da alkawuran da ke Littafi Mai Tsarki da suka shafi yadda za a magance matsalolin mahalli, ka karanta talifin nan, “Who Will Save the Earth?