WAƘA TA 103
Jehobah Ya Yi Tanadin Makiyaya
(Afisawa 4:8)
-
1. Allah ya ba mu makiyaya
Don su kula da mu.
Suna kafa misali mai kyau
Da za mu riƙa bi.
(AMSHI)
Allah ya yi mana tanadi,
Tanadin makiyaya.
Suna ƙauna da kula da mu,
Mu ƙaunace su sosai.
-
2. Makiyayan nan na da ƙauna
Da kuma sauƙin kai.
In mun fuskanci matsaloli
Suna kula da mu.
(AMSHI)
Allah ya yi mana tanadi,
Tanadin makiyaya.
Suna ƙauna da kula da mu,
Mu ƙaunace su sosai.
-
3. Suna yi mana ja-goranci
Don kar mu bijire.
Don mu ci gaba da bauta wa
Allahnmu koyaushe.
(AMSHI)
Allah ya yi mana tanadi,
Tanadin makiyaya.
Suna ƙauna da kula da mu,
Mu ƙaunace su sosai.
(Ka kuma duba Isha. 32:1, 2; Irm. 3:15; Yoh. 21:15-17; A. M. 20:28.)