WAƘA TA 127
Irin Mutumin da Ya Kamata In Zama
(2 Bitrus 3:11)
-
1. Ya Jehobah Allah, me nake da shi?
Mene ne zan ba ka domin ka ba ni rai?
Kalmarka tana sa in binciki kaina
Domin in san yadda zan faranta ranka.
-
2. Na yi alkawari zan bauta maka,
Ni ne na yi zaɓin don ina ƙaunar ka.
Da zuciya ɗaya zan bauta maka,
Ina so in faranta maka rai.
Ka taimaka mini, ka sa ni in san
Irin mutumin da kake so in zama.
Masu aminci, kana ƙaunar su sosai.
Ka taimaka min in zama mai aminci.
(Ka kuma duba Zab. 18:25; 116:12; Mis. 11:20.)