Aljanna Ta Kusa
Ka Saukar:
1. Za ka ji kukan tsuntsaye,
In gari na wayewa.
Kana tafiya a kwari
Kuma rana na haskakawa.
Ka ga duk masoyanka,
Wadanda suka mutu.
Allah ya kusan cika
Dukan alkawuransa.
2. Akwai gidaje a kwari
Akwai gida kan dutse.
Mutane suna wakoki
A gefen kogi mai guduwa.
Kayan gona sun yi kyau
Za mu fara yin girbi.
Allah ya kusan cika
Dukan alkawuransa.
3. Mu gaya wa duk mutane
Alkawuran Mulkin Allah.
Za a share hawayenmu
Za mu rayu har abada.
4. Mutane na farin ciki
Ga kuma kamshin fure.
Muna gai da masoyanmu
Bayan mun tashi lafiya lau.
Sai mu gode wa Jehobah
Domin yawan kaunarsa.
Duk alkawuran Allah
Sun yi kusan cikawa.
5. Zan yi murna a koyaushe,
Don na sake hadu da ke!
Mun yi kewar ki sosai fa
Ga shi kina tare da mu.
5. Sabuwar duniya
Muna jiran zuwan ta.
Mun san Allah zai cika duk
Alkawarin da ya yi mana.
Shi ya sa muke jimrewa
Don ladarmu ta kusa.
Muna jiran ladar nan,
Aljanna ta kusan zuwa.