Koma ka ga abin da ke ciki

Yin Aiki Tare da Shaidun Jehobah a Warwick

Yin Aiki Tare da Shaidun Jehobah a Warwick

Yadda ’yan’uwa suka ba da kansu da yardan rai don yin aikin gine-gine a Warwick ya sa mutanen da suke wajen mamaki sosai. Darektan wani kamfanin saka lif ya gaya wa wani ma’aikaci cewa: “Mutanenku suna yin aiki mai ban mamaki sosai. A yau, yawancin mutane ba sa ba da lokacinsu don yin aiki hakan.”

Sa’ad da darektan da kuma wasu suka fara jin cewa yawancin wadanda suke aikin gina hedkwatar Shaidun Jehobah a Warwick da ke jihar New York a Amirka sun ba da kansu da yardan rai ne, sai suka zata cewa wadannan Shaidun za su zo su yi aiki ranar Asabar da kuma Lahadi ne kawai. Amma sun yi mamaki da suka ga mutanen da suka bar ayyukansu kuma suka zo daga wurare dabam-dabam a kasar don su yi aiki na watanni, har ma shekaru.

A karshen shekara ta 2015, Shaidun Jehobah kusan 23,000 sun ba da kansu da yardan rai kuma sun yi aiki a Warwick tare da ’yan’uwan da ke Bethel a Amirka. Kari ga haka, mutane kusan 750 da suke aikin gine-gine da ba Shaidun Jehobah ba sun taimaka a aikin don a yi ginin bisa lokacin da aka tsara. Wadannan mutanen sun yi farin cikin yin aiki tare da Shaidun Jehobah.

Sun Jin Dadin Yin Aiki a Wajen

Manajan wani kamfanin sarrafa kayan yin taga da kuma bango ya ce: “Kowa da ya yi wannan aikin ya yi mamaki game da halin kirki na mutanen da suka yi aiki tare da su. Wannan ne ya sa yawancinmu muke so mu yi wannan aikin.”

Wani kamfani kuma sun kawo ma’aikata don su taimaka wajen gina gidajen zama. Sa’ad da kamfanin suka kammala aikinsu, ma’aikansu guda uku sun ce suna so su ci gaba da yin aiki a Warwick. Don haka suka bar aiki a kamfanin kuma suka ci gaba da aiki da wani kamfanin da ke aiki a wajen.

Halaye masu kyau na Shaidun ya taimaka wa wadannan ma’aikata su kasance da halin kirki. Wani mutum ya yi aiki da kamfanin da ke sa harsashi na gidajen. Bayan ya yi aiki na wasu watanni a Warwick, matarsa ta lura cewa halinsa da kuma yadda yake magana sun canja. Ta ce: “Maigidana ya canja gabaki daya!”

“Mata Shaidun Jehobah Za Su Zo”

Mata ne mutane da yawa a cikin Shaidun Jehobah da suka yi aiki a wurin gine-gine. Sun tuka motoci da share dakuna, kuma sun yi aikin sakatare. Ban da haka ma, sun ja-goranci motoci zuwa hanyar da za su bi, sun tuka da kuma yi aiki da manyan motoci da hada waya da saka bututu, da saka bangwaye, da aikin famfo, da kuma zuba kankare. Sun yi aiki sosai.

Wani ma’aikaci da ba Mashaidi ba da yake yin rufin gida ya lura cewa sa’ad da ma’auratan suke fitowa daga cikin mota, wasu sukan rike hanayen juna sa’ad da suke zuwa wurin aiki. Hakan ya ratsa zuciyarsa sosai. Kuma ya ga cewa matan suna aiki sosai. Ya ce: “Idan ka gan su, za ka yi zato cewa matan sun bi mazajensu ne kawai amma ba haka ba ne, matan suna aiki sosai. Na yi aikin gine-gine a wurare da yawa a jihar New York, amma ban taba ganin abu kamar haka ba.”

An yi sanyi sosai a shekara ta 2014 zuwa 2015, kuma hakan yakan sa mutum ya so ya zauna a gida maimakon ya je aiki. Wani Mashaidi da yake aiki tare da wadanda suke kula da aikin gina-ginen mai suna Jeremy ya ce: “A wasu ranakun da ake yin sanyi sosai, wani ma’aikaci da yake aiki tare da daya daga ciki kamfanonin gina-gine yakan tambaye ni, ‘Matanku za su zo aiki gobe kuwa?’

Sai in ce, ‘E.’

Sai ya tambaye ni kuma, ‘Har da wadanda suke aiki a waje?’

Sai in ce, ‘E.’

“Bayan haka, ya ce ya gaya wa mutanensa cewa ya kamata su zo aiki don mata Shaidun Jehobah za su zo!”

Masu Tuka Motoci Sun Ji Dadin Aikin

An yi hayar masu tuka motoci fiye da 35 don su rika kai ma’aikata wurin aiki da kuma masaukinsu.

Kafin wani matuki ya kai su wata rana, ya tashi tsaye kuma ya kalli Shaidun ya ce: “Ina jin dadin tuka ku sosai. Don Allah ku tura wa shugabanmu sako cewa ya bar ni in ci gaba da tuka ku. Na koyi abubuwa da yawa game da Littafi Mai Tsarki daga wurin ku. A dā ban san sunan Allah ba kuma ban san cewa duniyar nan za ta zama aljanna ba. Don haka ba na jin tsoron mutuwa kuma ba. Gaskiya na yi farin ciki sosai. Zan zo Majami’ar Mulki a lokacin da nake hutu.”

Wata Mashaidiya mai suna Damiana da ta yi aiki a Warwick ta ce: “Wata rana da muka shiga motarmu, sai direban ya ce yana da abin da yake so ya ce mana. Ya ce ya tuka Shaidu guda 4,000 zuwa wurare dabam-dabam da suke aikin gine-gine a jihar New York. Kari ga haka ya ce, ‘dukanku kuna da kasawarku amma duk da haka kuna aiki tare da hadin kai. Hakan abin sha’awa ne.’ Ya kuma ce yana jin dadin tattaunawa da mu.

“Bayan ya gama magana, sai wani Mashaidi a motar ya ce, ‘Kana jin dadin sa’ad da muke waka?’

“Ya yi dariya kuma ya ce, ‘Kwarai kuwa!

Mu rera waka ta 134?’” *

^ sakin layi na 23 Jigon waka ta 134 ita ce “Ka Ga Kanka Sa’ad da Kome Ya Zama Sabo.” Ka duba dandalin www.mr1310.com/ha a ƙarƙashin LITTATTAFAI > LITTATTAFAI DA KASIDU. Wakar ta kwatanta farin cikin da mutane za su yi a sabuwar duniya da Allah ya yi mana alkawarinta.