Zuwa Yin Wa’azin Bishara a Yankunan da Asalin ’Yan Kanada Suke
A kasar Kanada, akwai harsuna fiye da 60 da asalin ’yan kasar suke yi, kuma mutane wajen 213,000 sun ce daya daga cikin wadannan harsunan shi ne yarensu na asali.
Shaidun Jehobah da yawa sun koyi daya daga cikin wadannan harsunan don su iya koya musu gaskiya da ke cikin Littafi Mai Tsarki. A karshen shekara ta 2015, mutane fiye da 250 sun sauke karatu daga aji na koyan harsuna da Shaidun Jehobah suka gudanar.
Kari ga haka, Shaidun Jehobah sun fassara littattafai da ke bayyana Littafi Mai Tsarki da gajerun bidiyoyi zuwa harsuna takwas na asali mutanen Kanada, wato harsunan Algonquin da Blackfoot da Plains Cree da West Swampy Cree da Inuktitut da Mohawk da Odawa da kuma Northern Ojibwa. *
Mutanen da suke koyan harsunan nan sun ce yin hakan bai da sauki. Carma ta ce: “Sa’ad da na fara taimaka wa rukunin da ke fassara yaren Blackfoot, na ji kamar ina aiki a cikin duhu. Ban iya yaren sosai ba balle ma in karanta.”
Wani dan’uwa mai suna Terence, wanda yake aiki tare da rukunin fassara yaren West Swampy Cree ya ce, “Yaren yana da dogayen kalmomin kuma suna da wuyan furtawa.” Daniel, wanda yake hidima ta cikakken lokaci a tsibirin Manitoulin a lardin Ontario ya ce: “Babu kamus da kuma littattafai da yawa a yaren Odawa, amma idan kana so ka iya yaren sosai, ka nemi tsofaffin mutanen da suka iya yaren su koya maka.”
Shin akwai amfanin yin wannan aikin? Wata mata da take yaren Ojibwa ta ce, wannan aikin da Shaidun Jehobah suke yi ya sa sun bambanta da sauran addinai. Ta ce Shaidun Jehobah suna zuwa gidajen mutane kuma su karanta Littafi Mai Tsarki a yaren Ojibwa kuma hakan ya sa mutanen suna tattauna Littafi Mai Tsarki da su cikin kwanciyar hankali.
Wani mafasari da ya girma a karkarar Blood Tribe a jihar Alberta ya ce: “Na ga mutanen Blackfoot da yawa da suka ji dadin ganin littafi a yarensu kuma suka rungumi littafin suna cewa, ‘Wannan yaren na ne. Don ni aka buga wannan littafin!’ A yawancin lokaci ina ganin su suna zub da hawaye sa’ad da suke kallon wani bidiyo a yarensu.”
Wata mata da take yaren Cree ta ji dadin bidiyon nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? a yarensu. Ta ce ta ji kamar mahaifiyarta ce take mata magana.
Sun Yi Iya Kokarinsu
Shaidun Jehobah da yawa sun yi iya kokarinsu wajen zuwa irin wadannan wuraren don su gaya wa mutane game da sakon da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Terence da matarsa Orlean sun tuna da wani abin da ya faru kuma suka ce: “Muna cikin mutanen da suka yi tafiya a mota na awa 12 a wani hanyar kankara don mu yi wa’azi a wani wurin da ake kira Little Grand Rapids. Mutanen wajen sun saurare mu sosai!”
Wasu mutane sun bar gidajensu masu kyau kuma sun kaura zuwa wuraren da suke kusa da wadannan yankunan. Daniel da matarsa LeeAnn sun je tsibirin Manitoulin kuma sun yi wata uku suna wa’azin bishara a wajen. Sun ji dadin wa’azin sosai shi ya sa suka kaura zuwa wurin. Daniel ya ce: “Mun yi farin cikin ba da lokacinmu don muna son mutanen su yarda da mu kuma su ji bishara.”
“Saboda Ina Kaunarsu da Gaske”
Me ya sa Shaidun Jehobah suke yin iya kokarinsu don su yi wa mutanen da suke zama a irin wadannan yankunan wa’azi? Matar Bert mai suna Rose ta ce: “Da yake ni ’yar kasar ce kuma na shaida yadda bin ka’idodin Littafi Mai Tsarki yake amfanar mu, hakan yana motsa ni in taimaka wa mutane.”
Orlean ta ce: “Ina son mutanen Cree su sami damar sanin Mahaliccinmu kuma ya ja-gorance su. Taimaka musu su kusaci Jehobah kuma su iya shawo kan matsalolin da suke fuskanta babban gata ne a gare mu.”
Marc yana aiki tare da rukunin da suke fassara yaren Blackfoot. Me ya sa yake son ya taimaka wa mutanen da suke yaren Blackfoot? Ya ce: “Saboda ina kaunarsu da gaske.”
^ sakin layi na 4 Asalin ’yan Amirka ma suna yin wasu cikin wadannan harsunan.