Shin Shaidun Jehobah Suna Hada Bautarsu da Mutanen da Imaninsu ba Daya Ba?
Shaidun Jehobah suna jin dadin tattauna da mutane da suke da nasu addinin, amma ba sa hada bautarsu da mutanen da imaninsu ba daya ba. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Kiristoci na gaskiya “sun hadu suna rike da juna,” kuma abin da ya sa suka hadu da juna shi ne imaninsu. (Afisawa 4:16, Littafi Mai Tsarki, Juyi Mai Fitar da Ma’ana; 1 Korintiyawa 1:10; Filibbiyawa 2:2) Imani da ake nufin a nan, ba game da batutuwa irin su kauna da jinkai da kuma gafartawa ba ne. Abubuwan da muka gaskata da su suna cikin Littafi Mai Tsarki, kuma da ba sa cikin Littafi Mai Tsarki, da bangaskiyarmu za ta zama banza.—Romawa 10:2, 3.
Littafi mai tsarki ya nuna cewa idan mun hada bautarmu da mutanen da imaninsu ba daya ba ne da namu, hakan zai iya bata bangaskiyarmu. (2 Korintiyawa 6:14-17) Kari ga haka, Yesu bai bar almajiransa su hada bautarsu da mutanen da imaninsu ba daya ba. (Matta 12:30; Yohanna 14:6) Dokar da Allah ya bayar ta hanun Musa ma ta haramta wa Isra’ilawa hada bautansu da al’ummai da ke kewaye da su. (Fitowa 34:11-14) Daga baya, Isra’ilawa masu aminci sun ki su amince da tayi da aka yi masu wanda zai iya sa su hada kai da mutanen al’ummai.—Ezra 4:1-3.
Shin Shaidun Jehobah suna tattaunawa da mutanen da imaninsu ba daya ba?
E. A shekara ta 2022, mun yi amfani da awowi 1,501,797,703 wajen tattaunawa da mutanen da imaninmu ba daya ba. Kamar manzo Bulus, muna jin dadin sauraron abubuwan da “mutane da yawa” suka yi imani da su sa’ad da muke wa’azi. (1 Korintiyawa 9:19-22) Yayin da muke wa’azi, muna kokarin yin amfani da shawarar da ke Littafi Mai Tsarki da ya ce mu rika nuna “ban girma” ga mutane.—1 Bitrus 3:15.