Me Ya Sa Shaidun Jehobah Ba Sa Mai da Martani Kan Dukan Zargin da Ake Musu?
Shaidun Jehobah suna bin shawarar da Littafi Mai Tsarki ya bayar cewa, bai kamata mutum ya mayar da martani kan dukan ba’a ko zargin da aka yi masa ba. Alal misali, wani karin magana a cikin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wanda ya yi wa mai fariya horo, kunya yake jawo wa kansa.” (Misalai 9:7, 8; 26:4) Gwamma mu mai da hankali ga faranta wa Allah rai maimakon barin zargin da ake mana ya sa mu rika gardama da mutane.—Zabura 119:69.
Hakika, akwai “lokacin [yin] shuru da lokacin magana.” (Mai-Wa’azi 3:7) Muna amsa wa mutanen da suke so su san gaskiya, amma ba ma barin mutane su sa mu yi gardama da su. Kuma hakan ya nuna cewa muna bin koyarwar Yesu da misalinsa, da kuma na Kiristoci na farko.
Yesu ya ki ya ba Bilatus amsa a lokacin da Bilatus yake zarginsa. (Matta 27:11-14; 1 Bitrus 2:21-23) Hakazalika, Yesu bai mai da martani ba a lokacin da aka ce da shi dan giya da kuma mai hadama. Maimakon ya ba da amsa, ya bar salon rayuwarsa ya nuna ko zargin da ake masa gaskiya ne, kuma hakan ya yi daidai da wannan ka’idar: “Hikimar Allah, ta aikinta ne ake tabbatar da gaskiya tata.” (Matta 11:19) Amma a lokacin da ya kamata Yesu ya yi magana, ya mai da martani ga masu zarginsa ba tare da ya ji tsoronsu ba.—Matta 15:1-3; Markus 3:22-30.
Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa kada su bar zargin da ake musu ya sa su yi sanyin gwiwa. Ya ce: “Masu albarka ne ku lokacin da ana zarginku, ana tsananta muku, da karya kuma ana ambatonku da kowace irin mugunta, sabili da ni.” (Matta 5:11, 12) Amma Yesu ya ce a wasu lokuta zargin da ake mana zai iya ba mu damar ba da shaida game da Mulkin Allah. Idan hakan ya faru, Yesu zai cika wannan alkawarin da ya yi cewa: “Zan ba ku kalmomi da hikima yadda ko daya daga cikin masu gāba da ku ba zai iya juye maganar ko ya yi mūsun abin da kuka ce ba.”—Luka 21:12-15, Littafi Mai Tsarki, Juyi Mai Fitar da Ma’ana.
Manzo Bulus ya gargadi Kiristoci su guji yin mūsu da wadanda suke hamayya da su, domin ya ce, irin wannan mūsun “marasa amfani ne, banza ne kuma.”—Titus 3:9; Romawa 16:17, 18.
Manzo Bitrus ya ce Kiristoci su kāre imaninsu idan da hali. (1 Bitrus 3:15) Amma ya ce zai fi kyau idan Kiristoci sun yi hakan ta halinsu, maimakon su yi mūsu. Shi ya sa ya ce: “Bisa ga aikin kirki ku kwabe jahilcin mutane marasa hikima.”—1 Bitrus 2:12-15.